Wasannin da ke gaban Man United kafin Kirsimeti

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sabon kociyan Manchester United, Ruben Amorim zai ja ragamar wasa tara kafin bikin Kirsimeti, wanda ke fatan mayar da ƙungiyar kan ganiya.

Kociyan ya maye gurbin Erik ten Hag, bayan da United ke kasa taka rawar gani a wasannin kakar bana.

Cikin wasa tara da Amorim zai ja ragamar United kafin Kirsimeti, ya haɗa da karawar Premier biyar da Europa League biyu da kuma League Cup.

Kociyan zai fara da zuwa Ipswich Town a gasar Premier League ranar Lahadi daga nan ya karɓi bakuncin Bodo a Europa League ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba.

Wasa na uku United za ta kece raini da Everton a Premier a Old Trafford ranar 1 ga watan Disamba, sannan ta je Arsenal a karawar hamayya ranar 4 ga watan Disamba.

Ranar 7 ga watan Disamba Nottingham Forest za ta je United a gasar Premier ranar 7 ga watan Disamba, daga nan United ta je Viktoria a Europa League ranar 12 ga watan Disamba.

Za a buga wasan hamayya tsakanin Manchester City da United ranar 15 ga watan Disamba, sai United ta buga League Cup zagayen kwata fainal da Tottenham ranar 19 ga watan Disamba.

Daga nan United za ta fafata da Bournemouth a Premier a Old Trafford ranar 22 ga watan Disamba.

Premier League Lahadi 24 ga watan Nuwamba

  • Ipswich da Man Utd

Europa League Alhamis 28 ga watan Nuwamba

  • Man Utd da Bodo Glimt

Premier League Lahadi 1 ga watan Disamba

  • Man Utd da Everton

Premier League Laraba 4 ga watan Disamba

  • Arsenal da Man Utd

Premier League Asabar 7 ga watan Disamba

  • Man Utd da Nottm Forest

Europa League Alhamis 12 ga watan Disamba

  • Viktoria Plzen v Man Utd

Premier League Lahadi 15 ga watan Disamba

  • Man Cityda Man Utd

English League Cup Alhamis 19 ga watan Disamba

  • Tottenham da Man Utd

Premier League Lahadi 22 ga watan Disamba

  • Man Utdda Bournemouth