Hukumar Kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Nottingham Forest kan kutsen fili

Kutsen fili

Asalin hoton, OTHERS

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi Nottingham saboda magoya bayanta sun shiga fili a lokacin wasansu na kusa da karshe na gasar Championship a kakar da ta wuce.

A karawar Forest ta doke Sheffield United a bugun fanareti bayan wasan karo n abiyu da suka yi 3-3.

An daure wani mai goyon bayan Forest saboda ya yi wa kyaftin din Sheffield Billy Sharp.

Shi kuwa dan wasan Sheffield United Oli McBurnie zai gurfana a gaban sharia a watan Disamba bisa zargin ya kai hari kan wani dan kallo a lokacin kutsen filin.

Rhian Brewster kuwa na kungiyar ta Sheffield an yi watsi da tuhumar da ake masa a kan yamutsin a makon da ya gabata.

A takaddar tuhumar da aka gabatar a kan kungiyar ta Forest hukumar ta FA ta ce:

"An yi zargin cewa kungiyar Nottingham Forest ta kasa tabbatar da ganin cewa 'yan kallonta, da kuma dukkanin wasu mutane da ake nuna cewa magoya bayanta ne ko mabiyanta sun bi ka'ida.

Kuma sun ki kauce wa amfani da barazana da ko kuma dabi'a ta tayar da hankali yayin da suka yi kutse a filin a lokacin yamutsin."