Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin jaridar Thisday da Tinubu

An wallafa

Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin kamfanin Jaridar Thisday da darakatocin yakin neman zaben dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmad Tinubu.

Jaridar ta Thisday ta zargi daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaben Tinubu, Bayo Onanuga, da na tsare-tsare da kula da harkokin sadarwa Dele Alake da yunkurin rufe bakin 'yan jarida.

Thisday ta ce yunkurin da daraktocin yakin neman zaben na Tinubu ke yi ba shi da maraba da tsarin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na take hakkin fadar albarkacin bakin ‘yan jarida.

Sai dai kwamitin yakin neman zaben na Tinubu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana zargin na mai jaridar ta Thisday a matsayin wanda "ba shi da tushe ballantana makama."

Kwamitin yakin neman zaben na Tinubu ya ce babu wata kafar yada labarai da suka ware don su ci zarafinta.

Haka kuma ya zargi jaridar ta Thisday da yada wasu kasidu ta hanyar amfani da kalaman cin fuska da zagi ga dan takarar jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan ya nuna rashin kwarewarsu karara.

Zargin da Thisday ke yi

Editocin jaridar ta Thisday sun zargi daraktocin yakin neman zaben na Tinubu da yadda suka gaza amsa tambayoyin da aka yi musu a ganawa da 'yan jaridu sau hudu, maimakon su bayar da amsar tambayoyin da aka yi musu, ko su rubuto koke ga kamfanin sai suka zabi zargin kamfanin jaridar da nuna bangarancin ga dantakarar shugabancin kasar Bola Ahmed Tinubu.

"Sun yi kuskure. Fadar gaskiya da kawo rahoton abin da ya faru ko kadan ba bangaranci ba ne. Daraktocin biyu suna amfani da rashin kwarewar aiki da  ganganci da siyasantar da komai," in ji jaridar.

"Bayan fitar da sanarwarsu ta farko, mun yi watsi da su, sai suka sake fitar da ta biyu, ita ma muka yi burus, saboda ba ma son mu saka kanmu cikin harkokinsu na siyasa."

Editocin sun ce zarge-zargen da bangaren Tinubu yake yi musu sun kara zafafa, bayan da da aka wallafa labarin mutuwar wani makusancinsa, Mueez Adegboyega Akande, a shafin jaridarsu ta ranar 18 ga Watan Nuwambar 2022.

A cikin labaran an bayyana cewar hukumomin kasar Amurka na binciken mamacin da hannun kan zargin da ake yi wa dan takarar shugaban kasa na APC kan safarar miyagun kwayoyi a 1993.

Raddin da daraktocin kamfe na Tinubu suka yi

Daraktocin biyu na yakin neman zaben Tinubu sun zargi jaridar ta Thisday da cin zarafi da tursasa wa dan takarar shugabancin Najeriya a APC, Bola Tinubu, don ya halarci taron sauraro manufofin ‘yan takarar shugabancin kasar, duk da bayanin da kwamitin yada labaran takararsa ya yi cewar dan takarar tasu ba zai samu zuwa taron ba, bisa la’akari da yadda kafafen yada labaran ke amfani da kalaman da ba su dace ba a kansa.

“Dukkan kwamitin yakin neman zaben dan takararmu na da 'yanci su zabi tsare-tsaren da za su yi amfani da su wajen isar da sakonsu ko su yi magana kai-tsaye da 'yan Najeirya”.

Haka kuma sun nanata cewar ba za su taba yarda da zagon kasa, ko barazana da cin zarafin daga jaridar Thisday.

“Dan takararmu ba zai yarda wasu su bata masa suna ba, da dauke masa hankali daga abin da ke gabansa, don sun ga shi ne a kan gaba a cikin masu neman shugabancin Najeriya, shi ya sa suka fito da irin wannan yarfen na siyasa," in ji kwamitin yakin neman zaben Tinubu.