Zargin ɓatancin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin Tinubu da jam’iyyun PDP da LP

An wallafa

Zargin ɓata suna da ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kan abokan hamayyarsa na PDP da LP na cigaba da haifar da ce-ku-ce-ce tsakanin magoya bayan jam’iyyun.

Wannan batu ya fito fili ne lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya ce zai shigar da karar wasu kafofin yaɗa labarai da kuma jam’iyyun da ya zarga na yaɗa labaran karya domin ɓata masa suna da takararsa.

A karshen makon jiya ne aka rinƙa yawo da wata sanarwa da sunan hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, da ke cewa za ta binciki labaran da ke fitowa daga Amurka kan Bola Tinubu, da ke alaƙanta shi da harkar migayun kwayoyi.

Sai dai daga baya INEC ta fitar da sanarwa ta shafukanta na sada zumunta tana nesanta kanta da wannan sanarwa.

Lamarin ya harzuka jam’iyyar APC da tursasa mata fitar da sanarwa inda ta zargi PDP da LP da shirya mata manaƙisa.

Me takardun ke cewa?

Takardar da aka rinƙa yawo da ita na cewa wata kotu a Amurka ta kwace wasu dalolin Amurka daga asusun Tinubu a yankin arewacin Illinois kan zargin alaƙa da fataucin kwayoyi.

Sai dai kuma takardun ba su bada wasu bayanai ko tabbatar da cewa anyi wa Tinubu shari’a ba, ko kuma yana da alaƙa da wata kungiyar fataucin ƙwayoyi.

Takardun sun kuma nuna cewa anyi wannan shari’a ne shekaru 30 da suka gabata.

A cewar bayanan, wannan yanayi ne ya tursasa wa Tinubu sadaukar da kuɗaɗen da yawansu ya kai dala 460,000 a ɗaya daga cikin asusun bankunansa 10 da aka ce mallakar tsohon gwamnan Legas ɗin ne.

Sai dai kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya ce an ba da wadannan kuɗaɗen ne a matsayin haraji da Tinubu ya jima bai bayar ba.

Sannan kwamitin ya zargi maƙiya da abokan hamayya irin su PDP da LP da amfani da wannan dama wajen shirya labaran karya suna yaɗawa kan ɗan takarar shugabancin na APC.

Kwaimitin ya kuma yi barazanar daukar matakan shari’a kan kafofin yaɗa labaran da suka yaɗa wannan labari ba tare da tantace sahihanci ko gaskiyar zance ba.

APC na son ayi bincike domin gano wanda ya soma yaɗa sanarwar karyar da sunan INEC kan ɗan takararsu.

‘Babu wanda zai iya yi mana barazana’

Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta mayar da martani tana mai cewa tana da duk wata dama a doka ta kalubalantar takarar Bola Tinubu a APC, ciki har da cancantarsa a zaɓen 2023, la’akari da irin labaran da ake samu a kansa na saɓa doka da harkar migayun kwayoyi a Amurka.

A wani taron manema labarai, sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce Bola Tinubu bai cancanci wannan takarar ba sakamakon zarge-zarge da ke fitowa a kansa.

PDP ta ce zura wa ɗan takarar ido a wannan tafiya barazana ce ga tsarin ƙasar na dimukuraɗiya da mutuncinta a idon duniya.

Sannan ta kuma zargi cewa irin barazanar da suka fuskanta a gangamin yaƙin neman zaɓensu a Kaduna da Borno na nuna karara irin abin da APC za ta iya aikatawa.

‘Siyasar Najeriya ta gaji ɓatanci’

Masana harkoki siyasa irin su, Farfesa Abubakar Mu’azu, na Jami’ar Maiduguri ya ce dama siyasa ta gaji irin haka musamman a wannan gaɓa, don haka wannan bai zo masa da mamaki ba.

Farfesa Abubakar ya ce babban abin baƙin ciki a siyasar Najeriya shi ne yada 'yan siyasa ke kirkiro abubuwan da babu shi ko amfani da wata dama domin aibata mutum ko lalata takararsa ko da akwai gaskiya kan batun.

Ya ce duk waɗannan abubuwan neman mulki ne, wanda kuma ba wai zai taimakawa kasa ba. Don a duk lokacin da aka samu irin waɗannan zarge-zarge babu mai zama ya yi bincike ko nazari, kawai kambama batun za a rinka yi, domin cin ribar siyasa.

Masanin ya kuma ce abin takaici shi ne idan aka zo batun siyasa ba a mayar da hankali wajen lalubo abubuwan cigaban kasa ko kawo sauyi, abin da suka fi mayar da hankali shi ne binciken abubuwan ɓatanci ko ɓata takarar junansu.

Ya kuma kara da cewa ya kamata a ce mayar da hankali su ke yi kan ayyuka ko buƙatun jama’a, ko wa ya shirya kansa bisa cancanta da nazarin abubuwan da zai yi idan ya samu mulki.

Farfesa ya ce akwai tarin matsaloli a Najeriya, wanda ya kamata a ce su aka mayar da hankali ake kambamawa, sai da siyasar Najeriya ta gaji gaba da tozarta juna, shiyasa ake yin siyasar kamar yaƙi.