Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasa biyar kacal Chelsea za ta buga a cikin watan Janairu
Wasa biyar Chelsea za ta buga a watan Janairun 2025 da ya haɗa da huɗu a Premier League da FA Cup.
Ranar Litinin Chelsea ta yi rashin nasara 2-0 a gidan Ipswich Town a babbar gasar tamaula ta Ingila karawar mako na 19, wasan karshe da ta yi a 2024 kenan.
Hakan ya sa Chelsea mai maki 35 ta yi kasa zuwa ta huɗu a teburin Premier League, bayan cin wasa 10 da canjaras biyar da rashin nasara huɗu.
Ƙungiyar Stamford Bridge za ta fara wasa ranar 4 ga watan Janairu da zuwa Crystal Palace a Selhurst Park, wasan hamayya na ƙungiyoyin Landan.
Ranar 11 ga watan Janairu, Chelsea za ta karɓi bakuncin Morecambe a FA Cup, kwana uku tsakani ta yi wa Bournemouth masauki a Premier a Stamford Bridge.
Ranar 20 ga watan sabuwar shekara, Chelsea za ta fafata da Wolverhampton a gida daga nan ta yi wasan karshe a Janairun 2024.
Shi ne wanda za ta je Etihad ranar 25 ga watan Janairu, domin karawa da Manchester City mai rike da Premier na bara na huɗu a jere.
Ranar 18 ga watan Agusta, City ta doke Chelsea 2-0 a makon farko a Premier League a Stamford Bridge, kuma Erling Haaland da Mateo Kovacic ne suka ci ƙwallayen.
Wasannin da Chelsea za ta kara a 2025:
Premier League Asabar 4 ga watan Janairu
- Crystal Palace da Chelsea
English FA Cup Asabar 11 ga watan Janairu
- Chelsea da Morecambe
Premier League Talata 14 ga watan Janairu
- Chelsea da Bournemouth
Premier League Litinin 20 ga watan Janairu
- Chelsea da Wolves
Premier League Asabar 25 ga watan Janairu
- Man City da Chelsea