West Ham za ta tantance makomar Lopetegui kafin karshen mako

Asalin hoton, Getty Images
West Ham za ta fayyace makomar kociyanta, Julen Lopetegu kafin karshen mako.
Lopetegui yana fuskantar kalubale, bayan da Leicester City ta doke West Ham 3-1 ranar Talata a Premier a King Power.
Wata majiya ce ta sanar cewar mahukuntan ƙungiyar za su zauna taro a makon nan, domin fayyace makomar kociyan.
An ɗauki kociyan aiki kan fara kakar bana kan yarjejeniyar kaka biyu, wanda ya maye gurbin David Moyes.
Tun farko an sa ran Lopetegui, tsohon kociyan Sifaniya da Real Madrid zai taka rawar gani a West Ham, sai kuma ya ci karo da kalubale.
West Ham ta kashe sama da £120m wajen sayen ƴan wasa tara da cewar Lopetegui zai mayar da ƙungiyar gasar zakarun Turai, wadda ba ta je ta bara ba.
Kafin nan West Ham ta lashe Conference League karkashin David Moyes.
West Ham ta yi nasara ɗaya daga wasa shida tun bayan da ta doke Manchester United ranar 27 ga watan Oktoba - karawar da ta kai aka kori Erik ten Hag.
Rashin nasara da West Ham ta yi ranar Talata ya sa ƙungiyar ta yi kasa zuwa mataki na 14.
Har yanzu Niclas Fullkrug, wanda aka saya £27 bai buga Premier League ba, haka kuma minti 11 ɗan wasan Brazil, Luis Guilherme ya yi a wasa biyu da ya shiga canji.
Shi kuwa Crysencio Summerville baya kan ganiya.











