Arsenal ta yi tuntuɓe a hannun West Ham a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 a hannun West Ham United a wasan mako na 26 a Premier League ranar Asabar a Emirates.
West Ham ta ci ƙwallon ta hannun Jarrod Bowen daf da za su je hutun rabin lokaci, haka suka ci gaba har zagaye na biyu ba tare da Gunners ta zare ƙwallon ba.
Arsenal ta je da doke West Ham 5-2 a wasan farko a bana a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar 30 ga watan Nuwamba.
Tun kafin karawar ta Asabar, Arsenal ta yi nasara biyu a kan West Ham da cin ƙwallo 11, kenan Gunners ta doke West Ham har karo 37.
Ranar ta Asabar West Ham ta kawo karshen wasa 15 ba a yi nasara ba a kan Arsenal a Premier League, wadda ta ci wasa 10 da canjaras biyar.
Haka kuma an kawo karshen wasa 15 da Gunners ta yi ba tare da rashin nasara ba a gida.
Rabon da a doke Arsenal a Premier League a Emirates tun ranar Asabar 2 ga watan Nuwamba, inda Newcastle United ta yi nasara 1-0.
Da wannan sakamakon Arsenal tana ta biyun teburi da tazarar maki takwas, tsakani da Liverpool, bayan wasan mako na 26.
Ranar Laraba 19 ga watan Fabrairu ƙungiyar Anfield ta tashi 2-2 a gidan Aston Villa a gasar ta Premier League mako na 26.
Wasa biyar da ke gaban Arsenal:
Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu
- Nottingham Forest da Arsenal
Premier League ranar Lahadi 9 ga watan Maris
- Man Utd da Arsenal
Premier League ranar 16 ga watan Maris
- Arsenal da Chelsea
Premier League ranar Talata 1 ga watan Afirilu
- Arsenal da Fulham
Premier League ranar Asabar 5 ga watan Afirilu
- Everton da Arsenal
Wasa biyar da ke gaban Liverpool:
Premier League ranar Lahadi 23 ga watan Fabrairu
- Man City da Liverpool
Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu
- Liverpool da Newcastle
Premier League ranar Asabar 8 ga watan Maris
- Liverpool da Southampton
Premier League ranar Laraba 2 ga watan Afirilu
- Liverpool da Everton
Premier League ranar Asabar 5 ga watan Afirilu
- Fulham da Liverpool












