Copa del Rey: Barca za ta fuskanci Valencia a zagayen ƴan takwas

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona za ta je gidan Valencia a Copa del Rey zagayen kwata fainal, kamar yadda aka raba jaddawali ranar Litinin.

Barcelona ta kawo wannan matakin, sakamakon nasara a kan Real Betis 5-1 ranar Laraba 15 ga watan Janairu a zagayen ƴan 16.

Ita kuwa Valencia zuwa ta yi ta doke Ourense 2-0 ranar Talata 14 ga watan Janairu.

Valencia da Barcelona za su fuskanci juna a zagayen ƴan takwas ranar Laraba 5 ga watan Fabrairu a filin wasa da ake kira Mestalla.

Kafin nan Barcelona za ta je Benfica a Champions League ranar Talata 21 ga watan Janairu, sannan ta kece raini da Valencia a La Liga ranar Lahadi 26 ga watan Janairu.

Daga nan sai Barcelona ta karɓi bakuncin Alaves a La Liga ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu, sai kuma ta kara fuskantar Valencia a Copa del Rey ranar Laraba 5 ga watan Fabrairu.

A kakar nan Barcelona ta doke Valencia 2-1 a La Liga, inda Robert Lewandowski ne ya ci ƙwallayen ranar 17 ga watan Agustan 2024, shi ne labulen buɗe kakar 2024/25.

Ƙungiyoyin sun kara sau huɗu a baya a zagayen daf da karshe Copa del Rey, inda Barcelona ta kai zagayen karshe sau uku a 2017/18 da 2015/16 da kuma 2011/12.

Jadawalin kwata fainal a Copa del Rey:

  • Leganes da Real Madrid
  • Atlético Madrid da Getafe
  • Real Sociedad da Osasuna
  • Valencia da Barcelona