Babu shaidar ana bai wa ƙananan hukumomi kuɗinsu - CISLAC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Har yanzu masu fafutuka na ci gaba da ƙoƙarin ganin mahukunta a Najeriya sun mayar da hankali wajen aiwatar da hukuncin kotun ƙolin ƙasar, wanda ya nemi a bai wa ƙananan hukumomi ƴancin karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga gwamnatin tarayya, da kuma gudanar da su ba tare da katsalandan daga gwamnatocin jihohi ba.

A hukuncin da ta bayar ranar 11 ga watan Yulin 2024, kotun ƙolin ta Najeriya ta jaddada ƴancin cin gashin kai wajen tafiyar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi 774 na ƙasar.

Hukuncin wanda dukkan alƙalai bakwai na kotun ƙolin suka amince da shi ya tabbatar da ƙudirin da gwamnatin tarayya ta gabatar wa kotun ne, a ƙoƙarin ta na inganta harkokin mulki a matakin ƙananan hukumomin ƙasar.

Sai dai fiye da shekara ɗaya bayan wannan hukunci, ƙungiyoyi na ci gaba da bayyana damuwa kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙananan hukumomin na Najeriya, inda har yanzu ake zargin gwamnonin jihohi da hana shugabannin ƙananan hukumomi ƴancin karɓa da kuma tafiyar da kuɗaɗensu.

Awwal Musa Rafsanjani shi ne daraktan cibiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) mai rajin inganta ayyukan majalisun dokoki kuma shugaban reshen ƙungiyar Transperancy International a Najeriya, wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke da wannan damuwa.

Ya shaida wa BBC cewa ''har yanzu maganar nan da ake yi babu wani shaida kan cewa ƙananan hukumomin nan ana ba su kuɗaɗen su don su gabatar da aikace-aikacen da suke yi ba tare da sa baki ko kuma karkatar da waɗannan da gwamnoni suke yi ba.''

Rafsanjani ya ƙara da cewa wannan dalili ne ya sa CISLAC ta yi haɗin gwiwa da jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria da ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya (NULGE) da kuma sauran masu ruwa da tsaki, inda suka yi bita kan lamarin da kuma sanar da mafita.

''Ina ganin kamar su gwamnonin ba su son wannan tsari saboda suna ganin cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomin nan ba ƙaramin romo ba ne a gare su, saboda haka za su ci gaba da yin amfani da su.'' in ji Rafsanjani.

Me hukuncin kotun Ƙolin ya ƙunsa

A hukuncinta na watan Yulin bara, Kotun Ƙolin Najeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Najeriya su ne ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.

Kotun Ƙolin ta ƙara fayyace ƙarfin ƙananan hukumomi inda a hukuncin ta ce tana cikin matakan gwamnati – tarayya da jiha da kuma ƙaramar hukuma.

Kotun ta kuma ce gwamnatin jiha ba ta da ikon naɗawa da kuma tuɓe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi, dole sai ta hanyar zabe.

Duk da wannan hukunci dai, ƙungiyoyi irin su CISLAC na ganin cewa har yanzu gwamnonin na ci gaba da zama ƙarfen ƙafa ga ƙananan hukumomi a Najeriya.

''Amma abin da muke kira ga su shugabannin ƙananan hukumomi, duk wanda ya yarda aka yi abin da ba daidai ba, aka yi badaƙala, aka yi sace-sace ko kuma karkatar da kuɗi, to fa su tuna sunan su za a kira kuma su za su fuskanci hukunci idan suka yi ba daidai ba.'' in ji daraktan CISLAC.

Wane mataki ya kamata a ɗauka?

CISLAC ta ce akwai hanyoyin da suka dace a bi domin magance wannan matsala, kamar yadda suka cimma matsaya a taron masu ruwa da tsaki a game da batun.

''Dole ne a yi gyaran kundin mulkin ƙasa domin a tabbatar da cewa an shigar da tsarin aiwatar da wannan hukunci da kotun ƙoli ta bayar, ya zamo doka. Sannan na biyu muna so a bai wa shugabannin al'umma damar taka rawa a ƙananan hukumomi don a gina al'umma da kuma samun haɗin kai.

''Muna kira ga jama'a waɗanda ke da ƙwarewa su zo ƙananan hukumomi su yi aiki a wajen, kada a bar wajen a hannun waɗanda ba su san abin da suke yi ba.'' in ji Rafsanjani.

Daraktan na CISLAC ya ce hakan zai taimaka wajen ɓangaren hada-hadar kuɗi da ɓangaren haraji da kuma tsarin mulki.

Ya jaddada buƙatar jama'ar ƙasa su bada haɗin kai su koma ƙananan hukumomi a gina su don a samu ci gaba.