Uruguay ta yi waje da Brazil a Copa America

An wallafa

Uruguay ta kai daf da karshe a Copa America, bayan da ta doke Brazil da cin 4-2 a fenariti, bayan da suka tashi 0-0 a Las Vegas.

Manuel Ugarte ne ya zura na hudu a raga da ya kai Uruguay daf da karshe, bayan da aka tare ƙwallon Eder Militao sai ta Douglas Luiz da ta bugi turke a filin Allegiant.

Tawagogin biyu sun ɓarar da damarmaki, inda Uruguay, wadda Marcelo Bielsa ke jan ragama ta kare karawar da ƴan ƙwallo 10, bayan da aka bai wa Nahitan Nandez jan kati.

Da wannan sakamakon Uruguay za ta fuskanci Colombia, wadda ta caskara Panama, 5-0 a Charlotte, North Carolina.

An yi laifi 41 a karawar.

A ɗaya kwata fainal James Rodriguez ya ci ƙwallo, sannan ya bayar da biyu aka zura a raga, inda Colombia ta ci Panama 5-0 a State Farm Stadium in Glendale, Arizona.

Argentina, mai rike da kofin za ta fara buga daf da karshe ranar Talata, inda za ta fuskanci Canada a filin wasa na MetLife Stadium a New Jersey.