Ronaldo ya kafa tarihi na cin ƙwallo a ƙasashe huɗu

An wallafa

Gawurtaccen ɗan ƙwallon Portugal wanda a yanzu haka yake murza leda a Al- Nassr, Christiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi wajen zura ƙwallo a Saudiyya.

Ya zama ɗan ƙwallo na farko da ya ci ƙwallo 35 a gasar ƙwallon Saudiyya a kakar wasa ɗaya.

Ronaldo ya taimaka an ci ƙwallo 11 sannan ya zura ƙwallo 35 a cikin wasa 31 a kakar wasa ta bana.

Baya ga wannan tarihin da ya kafa a jiya daddare a wasan da Al Nassr ta doke Al Ittihad da ci huɗu da biyu.

Ronaldo mai shekaru 39 da haihuwa, ya kasance sanannen ɗan ƙwallo na farko a tarihi da ya ci ƙwallaye mafi yawa a kakar wasa ɗaya a ƙasashe huɗu daban-daban.

Ya yi wannan bajintar a Ingila da Sifaniya da Italiya da kuma Saudiyya.

A yanzu haka dai Ronaldo ya ci ƙwallo 64 a cikin wasa 69 a kungiyar Al Nassr tun bayan da ya raba gari da Manchester United a watan Janairun 2023.

Ɗan ƙwallon ya ci ƙwallo 765 a cikin shekaru 22 da ya kwashe ya na murza leda a ƙungiyoyin Sporting Lisbon, Manchester United, Real Madrid da kuma Juventus.

Shi ne ke riƙe da tarihin ɗan ƙwallon da ya fi kowanne ci wa ƙasarsa ƙwallo inda ya zura ƙwallo 128 a wasa 206 da ya buga wa Portugal.