Yadda ake tafka laifukan zaɓe a faɗin duniya

    • Marubuci, Issariya Praithongyaem
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Fiye da mutum biliyan huɗu ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a cikin wannan shekara a ƙasashe fiye da 60. Yayin da ake fargabar cewa dimokuraɗiyya na fuskantar barazana, masana sun yi bayanin hanyoyi da dama na aikata laifukan zaɓe da dabarun kauce musu.

Mene ne ingancin zaɓe?

Ingancin zaɓe shi ne idan sakamakon zaɓen ya martaba zaɓin mutane, kan abin da suka zaɓa, in ji Riccardo Chelleri, jami'in zaɓe a Tarayyar Turai.

Ya ce mutane na buƙatar yarda da ingancin zaɓen, kafin su fito su kaɗa ƙuri'a a ranar zaɓe.

“Dole a yi zaɓen a bayyane, babu ƙumbiya-ƙumbiya, ta yadda mutane za su san duka bayanan da suke buƙata,'' in ji Mista Chelleri, wanda ke a aiki a sashen lura da ayyukan zaɓe na Tarayyar Turai.

"Dole ne a shigar da kowa zaɓe. Ba wai maganar a bar masu zaɓe su kaɗa ƙuri'a ba ne kawai. Ana so a bar kowace jami'iyya ta shiga zaɓen, ta yi yaƙin neman zaɓe ba tare da riciki ba.''

Dakta Nic Cheeseman, masanin dimokuraɗiyya a jami'ar Birmingham da ke Birntaniya, ya ce bincikensa ya nuna cewa ingancin zaɓe a faɗin duniya na raguwa, inda ƴan takara da masu zaɓe ba sa samun damar gudanar da al'amuransu cikin ƴanci da walwala.

Akwai hatsarin cewa rashin ingancin zaɓe na neamn zama wata al'ada, kamar yadda ya yi bayani.

“Babu wani zaɓe da za a ce shi ne ya fi, amma yawan ingancinsa na taimaka wa masu kaɗa ƙuri'a wajen zaɓar shugabanni tare da tabbatar da cewa sun yi abin da ya kamata,'' in ji Dakta Cheeseman.

Ta ya ake yaudarar masu kaɗa ƙuri'a?

Ana fara shirye-shiryen zaɓe aƙalla kwana ɗaya bayan gudanar da wani zaɓen, domin tunkarar na gaba.

Don haka masana suka ce ana yaudarar masu kaɗa ƙuri'a a kowane lokaci a wannan tsakani.

“Ƙaramin ƙwaro ne ke maguɗi a ranar zaɓe. Ƙwararrun kan shirya maguɗinsu aƙalla shekara guda kafin ranar zaɓe,'' in ji Dakta Cheeseman.

Dabarun maguɗi sun haɗa da yadda gwamnati ke amfani da jami'an tsaro wajen razanar da ƴan'adawa, tare da hana kafofin yaɗa labaran gwamnati yaɗa sakonnin ƴan'adawa, da kuma saka ranar zaɓen da za ta yi daidai da muradun jam'iyya mai mulki.

“Da dama abin da ke faruwa shi ne, waɗanda ke kan mulki ne ke naɗa alƙalai waɗanda a lokuta da dama, waɗanda suka naɗa sun ke yin tasiri a ayyukansu, don haka da wuya ƙalubalantar zaɓen a kotuna ta yi nasara, in ji Mista Chelleri.

Duk da ƙaruwar fargabar, wannan abu ba ya faruwa a Amurka.

Duk da cewa Donal Trump ne ya naɗa alƙalai uku na kotun ƙolin ƙasar a lokacin da yake shugaban ƙasar, amma sun yanke hukuncin da ya ba shi rashin gaskiya a ƙarar da ya shigar domin ƙalubalantar nasarar Joe Biden a zaɓen 2020.

Wata dabarar ta maguɗin zaɓe ita ce rage yawan mazaɓu, inda ake rage yawan mazaɓu domin taimaka wa wasu gungun mutane.

Jam'iyya mai mulki, ko gwamnati kan yi amfani da kuɗin gwamnati wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, da kuma yaɗa labaran ƙarya, domin rage wa zaɓen inganci, ko sayen ƙuri'a.

“A Amurka, akwai babbar damuwa kan matsalar rage girman mazaɓu da zaluntar masu zaɓe tare da yaɗa labaran ƙarya,'' in ji Dakta Cheeseman.

Akwai babban hatsarin cewa labaran ƙarya, maguɗin zaɓe da rigingimun siyasa za su iya aukuwa a lokacin zaɓukan El Salvador da India da Sri Lanka, in ji shi.

Me ne maguɗin zaɓe?

Yunƙuri ne na sauya sakamakon zaɓe bayan kammala kaɗa ƙuri'a.

Wannan ya haɗa da dangwala ƙuri'u a wani wuri, tare da jefa su cikin akwatin zaɓe, da sauya alƙaluma bayan kammala zaɓe ko kuma lalata akwatunan zaɓe don lalata ƙuri'un ƴan'adawa.

Kusan kwana uku da aka ɗauka ana gudanar da zaɓen ƴan majalalisa a 2021 a Rasha, an yi ta samun zargin tafka maguɗin zaɓe, ciki har da cushen ƙuri'u a akwatunan zaɓe da razana masu sanya idanu a zaɓen.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan intanet ya nuna yadda mutane ke cusa ƙuri'un da aka kaɗa cikin akwatunan zaɓe.

To amma gwamnatin Rasha ta ce ba a samu rahoton 'karya doka a zaɓen ba''.

Dakta Cheeseman, wanda ke cikin waɗanda suka rubuta littafin ''Yadda ake Maguɗin Zaɓe.''

Ya ce ana aringizon ƙuri'u daga ko'ina, ciki har da ƙasashen da tsarin zaɓukansu ya cigaba.

A waɗannan ƙasashen, masu sanya idanu na cikin gida, da wakilan jam'iyyu kan je rumfunan zaɓe, don tattara alƙaluman zaɓen da kansu.

Dakta Cheeseman ya ce zaɓen shugaban ƙasar Ghana na 2016, inda jam'iyyun adawa ke amfani da wayoyi wajen tattara sakamakon zaɓen.

Haka ma a Zambiya a shekarar 2021, masu sanya idanu na cikin gida da ƙungiyoyin coci, sun yi aiki da ƙungiyoyin duniya wajen tattara matsalolin da aka samu. Hakan ya tilasta wa hukumar zaɓen wajen sakin sakamakon irin nasu.

Don haka, wannan abu ya yi tsauri cikin fiye da shekara 10, in ji Dakta Cheeseman.

Ya ƙara da cewa gwamnati a hukumance ta zartar da dokoki don taƙaita ayyukan ƙungiyoyin fararen hula a lokutan zaɓe.

Masu sanya idanu a zaɓen, ba su samu damar ganin komai ba sai ƙarshen zaɓukan, in ji Mista Chelleri, kuma hakan ba zai hana maguɗi ba a farkon tsarin.

Shin jam'iyyun adawa na maguɗi?

Su ma jam'iyyun adawa kan yi nasu dabarun don gudanar da maguɗi, in ji Dakta Cheeseman.

“Yanzu kamar Donald Trump, wanda a yanzu ke cikin ƴan'adawa, kan yi amfani da zarge-zargen, wasu gaskiya ne wasu kuma ba gaskiya ba ne domin yin amfani da su a ƙoƙarinsa na rage ƙimar gwamnati,'' in ji shi.

Shin dimokuraɗiyya na cikin hatsari?

“Kada mu yaudari kanmu. Dimokuraɗiyyar duniya na cikin lokaci na hatsari,'' in ji Riccardo Chelleri, jami'in zaɓe a Tarayyar Turai.

"Ina tunanin an samu raguwar ƙimar dimokuraɗiyya cikin shekara biyar da suka gabata.”

Ya ce abubuwan da ke janyo haka sun haɗa da rashin ƙarfin tattalin arziki, da tasirin shafukan sada zumunta ta hanyar yaɗa labaran ƙarya.

Dakta Cheeseman ya ce makomar dimokuraɗiyya ta dogara ne kan sakamakon zaɓukan wannan shekara.

“Idan mutane na gudanar da dimokuraɗiyyar da koyaushe ake murɗe sakamakon zaɓe, to ko ba jima, ko ba daɗe za su sha mamaki'', in ji shi.