Najeriya ta ci Kamaru ta samu gurbin gasar kofin duniya

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Najeriya ta doke ta Kamaru da ci 1-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Afirka da suka kara ranar Alhamis.

Minti 11 da komawa zagaye na biyu Falcons ta ci kwallo ta hannun Rasheedat Ajibade a wasan na hamayya da suka kara a Casablanca.

Da wannan sakamakon Super Falcons ta samu kai wa zagayen daf da na karshe ta kuma samu gurbin shiga gasar kofin duniya da za ta wakilci Afirka a badi.

Wannan shi ne karo na 12 da Supeer Falcons ta kai daf da karshe a gasar kwallon kafa ta mata ta cin kofin Afirka.

Haka kuma karo na tara a jere da Falcons za ta wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da za a yi a 2023.

Tun farko an tsara cewar duk kasahe hudun da suka kai daf da karshe a wasannin bana, za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da za a yi a New Zealand da Australia.

Koda yake an yi waje da Indomitable Lionesses daga gasar kofin Afirka, sai dai tana da damar samun gurbin kofin duniya a badi da za a tantance ranar Lahadi.

Bayan da Afirka ta Kudu ta doke Najeriya a wasan farko, daga nan Falcons ta kara sa kaimi, inda ta doke Burundi da kuma Botswana.

Falcons za ta buga karawar daf da karshe da mai masaukin baki Morocco.