Me zai faru a wasan Man City da Arsenal a Premier?

An wallafa

Manchester City da Arsenal za su barje gumi a wasan mako na 33 a gasar Premier League ranar Laraba a Etihad.

Arsenal tana matakin farko a kan teburin Premier League mai maki 75, ita kuwa City mai kwantan wasa biyu tana da maki 70 mai biye da Gunners.

Kungiyar Etihad ce mai rike da Premier League, wadda ta dauka a bara ranar karshe da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu.

Kawo yanzu City ta ci Arsenal karawa biyu a bana - ta fitar da Arsenal daga FA Cup da cin 1-0 da kuma 3-1 a Etihad a Premier League.

City ta lashe dukkan wasa shida na Premier League a gida a karawa da Arsenal karkashin Pep Guardiola.

Haka kuma Gurdiola ya ja ragamar City ta zura kwallo a ragar Gunners 17-3 cikin fafatawar shidan.

Rabon da City ta yi rashin nasara a gida a hannun Gunners tun 2-0 a Janairun 2015.

Kwallo uku kacal Arsenal ta zura a ragar City a karawa 10 baya a Premier League da kasa cin kwallo a wasa bakwai.

Liverpool ce kadai ta ci Arsenal karo uku a kakar tamaula daya, 1994-95, 1996-97 da kuma 2021-22.

Arsenal na fatan lashe Premier League a karon farko tun bayan 2004 karkashin Arsene Wenger.