Chelsea ta nada Graham Potter a matsayin sabon kocinta

Graham Potter ya fara kwallo ne a  Birmingham City a 1992

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta nada Graham Potter a matsayin sabon kocinta bayan korar Thomas Tuchel da ta yi.

Potter ya bar kungiyarsa ta Brighton da take buga Premier domin fara aikinsa wanda ya sanya hannu akai na tsawon shekara biyar.

Mai shekara 47 ya ce yana "matukar farin ciki da murna da zama kocin Chelsea".

Wasan farko da Potter zai buga a gidan Fulham ne wanda shi ma wasan hamayya ne, a ranar Asabar da misalin karfe 12:30.

"Mun yi farin cikin kawo Graham Chelsea," in ji shugaabn kungiyar Todd Boehly.

"Bayan kawai cewa yana da basira ba ne a yadda yake tafiyar da wasanninsa, yana da kuma kwarewa wajen alaka mai kyau da yan wasa ta yadda za kai Chelsea ga nasara.

"Ya yi matukar tasiri a tsohuwar kungiyar da ya jagoranta dan haka muka kawo shi nan muma ya sauya mana kungiyarmu."