Sauyin yanayi: Labarin tsuntsayen da suka jinkirta yin kwai da mako uku

Day-old great tit nestlings in the palm of a scientist's hand
Bayanan hoto, Masana kimiyyan na da izinin leka dukkan shekar da ke dajin domin taimaka wa tsuntsayen
    • Marubuci, Daga Victoria Gill
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan Kimiyya
  • An wallafa

"A wani bangare na wannan dajin, tsuntsaye sun jinkirta yin kwai da mako uku," inji Dakta Ella Cole ta Jami'ar Oxford.

Wannan kwararriyar masaniya a fannin nazarin rayuwar tsuntsaye na zagayawa da ni ne a wani wuri na musamman - wato dajin Wytham da ke Oxfordshire; daya daga cikin dazukan da aka fi gudanar da bincike cikinsa a duniya.

Wannan shekarar ta bana ta kasance ta 75 da aka fara wani bincike da ke nazari kan wasu tsuntsaye nau'in great tits a dajin.

Wannan dadadden bincike ne irin wanda ba a saba ganin irinsa ba a duniya.

A bisa wannan nazarin na gomman shekaru ne da ya biyo bayan yin kwai na shekara zuwa shekara - wanda ake makala wa tsuntsaye alamu da kuma kirga su, da rubuta ainihin lokacin da suke yin kwai da ranakun da suke kyankyashe kwayayen - shi ne ya bayyana sauyin da ake magana a kai a wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga sauyin yanayi.

"Tsuntsayen na tits a nan na iya gane lokacin da sauran halittun da suke ci a matsayin abincinsu," kamar yadda Dakta Cole ta bayyana.

"Tsarin lokacin da suke samun abincin da ke sa su yi kwai ya sauya da wasu makonni."

Dr Ella Cole in Wytham Wood

Asalin hoton, Victoria Gill

Bayanan hoto, An ware wannan dajin ne ne domin binciken kimiyya

Alkaluman nazarin da aka yi na shekara 75:

  • 700-800 - yawan shekarar da aka kidaya cikin kowace shekara
  • 10,000 - yawan tsutsotsi nau'in caterpillar da tsuntsayen da ke cikin makonni biyu gabanin su fara kwancin yin kwai
  • 350 - yawan kasidun da aka samar na nazarin da ake yi a wannan dajin na Wytham kan tsuntsayen na tits.

Iyalan wani gida a yankin ne suka sallamar da wurin ga Jami'ar Oxford a 1942 domin ta gudanar da binciken kimiyya a wurin.

Lallai masu nazarin sun taka rawar gani kan aikin da aka sa su. A daji mai fadin eka 800, a yanzu akwai sheka kimanin 1,200 na musamman da aka samar, kuma wadansu sun kasance a wurin tun 1947.

Akwai alamun nazarin kimiyya a ko'ina ka duba - kana iya ganin wasu jakunkunan da aka makala wa raga domin kama tsutsotsi, baya ga tarkon da aka kafa a kasan wasu rumfuna.

Great tit fledgling at Wytham

Asalin hoton, University of Oxford

Bayanan hoto, Nazarin ya duba Binciken ya duba rayuwar tsuntsaye na shekaru 75

Sai dai nazari mafi dadewa da aka yi a dajin na Wytham shi ne kan tsuntsun mai suna 'great tit'.

Tsuntsaye ne da ke da gajeruwar rayuwa a duniya - inda ba sa wuce shekara biyu daga haihuwa zuw amutuwarsu - saboda haka nazarin shekara 75 ya duba rayuwar jerin tsuntsaye 40 ke nan.

Irin bayanan da aka tara ya smaar da wani ilimi mai zurfi kan rayuwar tsuntsayen a wannan wurin.

Bluebells at Wytham
Bayanan hoto, Wadannan furannin samfurin Bluebells alama ce ta yadda dajin ya dade babu wanda ya dame shi da noma ko farauta na lokaci mai tsawo

Wani bincike da aka yi a shekarra 2017 wanda ya kwatanta tsuntsayen dajin na Wytham da wasu tsuntsayen da ke kasar Netherlands, kuma ya nuna cewa tsuntsayen na Wutham da ke Birtaniya sun sauya ta hanyar samun dogayen bakuna, lamarin da ya basu damar cin abinci sosai.

Sauyin yanayi ya sa an mayar da hankali sosai kan yadda tsarin rayuwa ke sauyawa - wanda ya ba masana kimiyya damar gane yadda sauyin yanayin ke tasiri kan rayuwar halittu kamar tsuntsayen na great tits.

Babu alamar za a daina gudanar da wannan binciken, ko ma a rage girmansa - domin akwai wsu masana kimiyya da aikinsu ne kawai su kula da shekar tsuntsaye kimanin 800 a karshen kowane yanayin sanyi, wato gabanin zuwan yanayin zafi ke nan. Kuma a kowace shekara, akan kara gane yadda rayuwar tsuntsayen ke kasancewa.