Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Modric, Gavi, Mane, Haaland., Nkunku da Lewandoski

An wallafa

Liverpool na shirin ba dan wasan Senegal Sadio Mane sabon kwantiragi. Kwantiragin dan wasan mai shekaru 30 a halin yanzu zai kare ne cikin watanni 12. (Football Insider)

Liverpool na son dan wasan Barcelona da Spain Gavi, mai shekara 17 ya koma kuniyar a bazara (Sport - in Spanish)

Shugaban Borussia Dortmund Sebastian Kehl ya ce Manchester City ba ta amince da cinikin dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21 ba (Mail)

Shugaban Bayern Munich Oliver Kahn ya ce kungiyar ba ta da karfin siyan Haaland. Kahn ya kuma tabbatar da cewa kulob din yana tattaunawa da dan wasan Poland Robert Lewandowski, mai shekara 33. (Sport, via 90 Min)

West Ham na shirin neman dan wasan bayan Manchester United Di'Shon Bernard. Dan wasan mai shekaru 21 a halin yanzu yana zaman aro a Hull. (Mirror)

Tottenham na sa ido kan tsohon dan wasan tsakiya na Brentford Christian Eriksen, mai shekara 30. Dan kasar Denmark din yana son komawa Spurs (Football Insider)

Arsenal na shirin dauko dan wasan Lille dan kasar Kosovan Edon Zhegrova, mai shekara 23. (Sky Sports)

Duk da haka Gunners na iya rasa dan wasan tsakiyar RB Leipzig Christopher Nkunku wanda yanzu haka Inter Milan ke matsawa lamba (Gazzetta dello Sport)

Dan wasan gaban Everton da Brazil Richarlison, mai shekara 24, ya shaida wa wakilansa su nemo masa sabon kulob. (Football Insider)

Newcastle ta shirya tsaf domin sake zawarcin dan wasan bayan Torino Gleison Bremer. Dan kasar Brazil din mai shekaru 25 kuma ya ja hankalin Arsenal da Tottenham. (Tuttomercato)

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce dan wasan tsakiya na kasar Croatia, Luka Modric zai bar kungiyar. Ana danganta dan wasan mai shekaru 36 da komawa Newcastle da Manchester City. (Sun)