Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Raphinha, Azpilicueta, Osimhen, Depay, Rice, Schjelderup

Barcelona ta kammala yarjejeniyar dauko dan wasan gaba na Brazil wato Raphinha, mai shekara 25, daga kungiyar Leeds United a kakar bana. (Sport - in Spanish)
Har wa yau Barcelona ta shirya tsaf domin sakin 'yan wasa bakwai a wannan kakar, saboda tana kokarin dauko dan wasan Chelsea, mai tsaron baya kuma dan Sifaniya Cesar Azpilicueta, mai shekara 32, da dan wasan tsakiya na Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, wadanda duka ake batun za su je Nou Camp. (AS - in Spanish)
Tottenham na sahun gaba wajen yunkurin dauko dan wasan gaba na Netherlands Memphis Depay, mai shekara 28, daga Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, mai shekara 23, na sahun gaba da ake ganin zai iya zama kaftin din Ingila, kamar yadda shugaban Three Lions, Gareth Southgate ya fada. (Mirror)
Real Madrid na shirin sayo mai tsaron bayan Arsenal da Scotland Kieran Tierney, mai shekara 24 kan fam miliyan 50. (Sunday Post)
Napoli za ta sayo mai kai hari kuma dan wasan Najeriya Victor Osimhen kan fam miliyan 83. (Corriere dello Sport, via Sun)
An bai wa masu kungiyar Chelsea wa'adin 11 ga watan Afirilu mai zuwa su mika matsayarsu ta karshe na kudin kulob din. (talkSPORT)
Dan wasan Norway da tauraronsa ke haskawa Andreas Schjelderup, mai shekara 17, ya ce ya ki amincewa da damar da ya samu ta rattaba hannu kan jarjejeniya da Liverpool, sai dai dan wasan tsakiyar ya bar kofa a bude kan wata dama nan gaba. (Liverpool Echo)
Kungiyoyin gasar Firimiya sun dana tarko kan dan wasan Arsenal da Ingila Ainsley Maitland-Niles, mai shekara 24, wanda ba a da tabbacin Roma za ta ci gaba da rike shi aro fiye da kakar wasannin bana. (Mirror)










