Roman Abramovich: An bukaci a kwace kadarorin mai kungiyar Chelsea

An wallafa

Dan majalisar wakilan Burtaniya bangaren adawa Chris Bryant ya bukaci gwamnati da ta kwace kadarorin mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich.

Dan majalisar ya ce ya samu wasu bayanan sirri da ke nuna cewa biloniyan dan kasar Rasha ya aikata wasu abubuwa da bai dace ace yana zaune Burtaniya ba.

Rahotanni sun ce ana zargin mai kulob din Chelsea din da aikata wasu abubuwa masu alaka da cin hanci, kuma ba tun yanzu bayanan suka fita ba amma hukumomi sun kau da kai.

To sai dai fadar Downing Street ta ce ba haka nan kawai za ta dauki mataki ba don wani mutum ya yi irin wannan zargi.

Kazalika mai magana da yawun Mr Abramovich har yanzu bai yi martani ba kan zargin.

A farkon mako gwamnatin Burtaniya ta sanar da shirin kakaba takunkumi ga wasu biloniyoyi uku da ke da alaka da Shugaba Vladimir Putin, a wani bangare na martani ga Rasha na shirin kutsawa Ukraine.

Sai dai ba a bayyana sunayen mutanen ba, duk da Roman Abramovich na daga cikin hamshakan attajiran da ke da alakar kud-da-kud da Vladimir Putin.

Da yake magana a zauren majalisa Mr Bryant ya bukaci gwamnati da ta dauki matakin kan Mr Abramovich, da ya hada da kwace kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga zama mallakinsa da kuma kwace wasu kadarorinsa.

A cewar Mr Bryant ''tabbas bai kamata a ce Mr Abramovich ya cigaba da mallakar kungiyar kwallon kafa ba a wannan kasa.''

''Ba makawa ya kamata mu duba yiyuwar kwace wasu daga cikin kadarorinsa, da suka hada da gidansa na fam miliyan 152.'' In ji Mr Bryant