Rikicin Ukraine da Rasha: Hotunan yadda kungiyoyin kwallon kafa a Turai suka nuna goyon baya ga Ukraine

An wallafa

Yayin da Ukraine ta fara fuskantar hare-hare daga Rasha, kungiyoyin kwallon kafa da dama sun nuna goyon baya ga Ukraine a lokacin wasanni Zakarun Turai na Europa da aka buga Alhamis da daddare.

Wasu daga cikin yan wasan da suka ci kwallo sun nuna riga dauke da kalaman bukatar zaman lafiya a Ukraine.

Ga jerin hotunan yadda yan wasan suka nuna goyon bayansu kan abinda ke faruwa a Ukraine din.