World Cup: Yan kwallo a kasashen duniya na adawa da yiwa gasar garambawul

An wallafa

Wani bincike da kungiyar kwararrun yan wasa ta duniya ta gudanar ya nuna cewa kashi 75 na yan kwallo maza, basu yadda a mayar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekara biyu ba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ce ta gabatar da wani shiri na mayar da gasar duk bayan shekara biyu a maimakon hudu, da nufin gyara jadawalin yadda gasussukan kwallon kafa ke gudana a fadin duniya.

Binciken ya ji tabakin yan wasa sama da 1,000 daga kasashe sama da 70.

Binciken ya kuma gano cewa yan wasan sun fi girmama gasar kofin duniya da kuma gasussukan cikin gida da suke bugawa.

Kashi 77 na yan wasa a Turai da Asiya sun goyi bayan a bar gasar duniyar yadda take, yayin da kashi 49 a Amurka da Afrika suma suka goyi bayan a cigaba yadda ake.

To amma duk da haka kungiyar ta Fifpro ta yadda cewa akwai bukatar fito da hanyoyin bunkasa kwallon kafa a tsakanin kasashe ta hanyar shirya gasussuka.

A cewar Janar Sakatare na Fifpro Jonas Baer-Hoffman ''binciken da muka yi kan yan wasa ya nuna cewa sun zabi a buga gasar cin kofin duniya ne duk bayan shekara hudu.

Shima Shugaban hukumar da ke shirya gasar turai Aleksander Ceferin ya ce kasashen turan za su kauracewa bukatar buga gasar cin kofin duniyar duk bayan shekara biyu''.

Sai dai a watan Disamban 2021 Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya ce yana da kwarin gwuiwa cewa za a samu hadin kan masu ruwa da tsaki wurin ganin an yiwa gasar garambawul.