Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
APC za ta fara zaman sasanta `ya`yanta
A ranar Litinin ne kwamitin sulhu na jam`iyyar APC mai mulki zai fara zaman sasanta `ya`yanta da ke kukan ba a kyauta musu a zabukan shugabannnin jam`iyyar da aka gudanar a matakai daban-daban.
Kwamitin zai fara ne da jihar Kano da ke shiyyar arewa maso yammacin kasar.
Shugaban kwamitin Senata Abdullahi Adamu ya ce za su fara da jihar Kano ne saboda muhimmancin da take da shi a cikin jam`iyyar APC.
"Kano ta na cikin jihohin da suka ba mu kuri'u na arziki, wadanda suka kai jam'yyarmu ga nasara, shi yasa mu ka cewa dole ne mu fara gyra a Kano" in ji shi
Sai dai kwamitin ya ce bai riga ya tattance bangarorin da ya ke da niyyar ganawa da su ba amma ya ce ya samu korafe -korafe a rubuce musaman kan zabukan da aka yi na ward-ward da na kananan hukumomi da kuma jihohi.
Sanata Abdullahi Adamu ya kuma kara da cewa: "Akwai wadanda suka yi kara ko suka koka kan abubuwan da aka gudanar a wadanan zabukan da aka yi, wanda kuma dole ne mu je mu duba mu ga menene gaskiyar abinda ya faru da kuma hanyar da za a bi domin a yi gyrar da kowa zai ce an gode Allah an samnu masallaha" .
Abinda ya haifar da baraka a Kano
Bangaren tsohon gwamnan jihar Kano sanata Ibrahim shekarau ya zargi da bangaren gwamna Ganduje da rashin damawa da su a cikin harkar siyasar kasar.
Sai dai zargi ne da bangaren Ganduje ya musanta.
Wannan alamari ya sa bangarorin biyu sun gudanar da zabukan shugabbanin jam'iyyar daban-daban inda kowane bangare ya zabi jagoransa.
Wannan rikici cikin gida ya sa wasu masu sharhi na ganin cewa abu ne da zai iya yin illa ga jam'iyyar APC mai mulki a zaben shekarar 2023 idan ba ta dauki matakin maganceta ba.
I