Kasuwar ƴan ƙwallo: : Kociyoyi na ci gaba da barranta kai da United, makomar Sanches, da Umtiti da sauran su

Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mauricio Pochettino
An wallafa

'Yan wasan Paris St-Germain sun yi imanin kociyan kungiyar Mauricio Pochettino zai tafi Manchester United kuma suna sa ran Zinedine Zidane ya maye gurbinsa. (Marca, in Spanish)

Dole ne United ta biya Yuro miliyan 10 (£8.4m) idan tana son ta raba dan kasar Argentinan mai shekara 49, da PSG. (Madubi)

Kociyan Sevilla Julen Lopetegui, mai shekaru 55, ya bayyana rade-radin da ke alakanta shi da Manchester United a matsayin shirme. (Mirror)

Shugaban Manchester United Ed Woodward yana tunanin jinkirta barinsa Old Trafford don taimakawa nemo magajin Ole Gunnar Solskjaer. Mai shekaru 50 a duniya zai bar aikinsa a kungiyar a karshen wannan shekarar. (Sky Sports).

Mo Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mo Salah

Dan wasan gaba na Liverpool Mo Salah ya kusa rattaba hannu kan sabon kwantiragi na dogon lokaci a kungiyar. Dan kasar Masar, mai shekara 29, zai shiga shekarar karshe ta kwantiraginsa a bazara mai zuwa, inda kulob din ke son kammala sabunta masa wa'adi. (Team Talk)

An ce tsohon kocin Newcastle United Steve Bruce yana matukar sha'awar aikin kocin Manchester United na gajeren lokaci. Baturen mai shekaru 60 ya buga wa United wasanni sama da 300 a matsayin dan wasa. (The Athletic )

Arsenal ba za ta tattauna sabon batun sabuntawa dan wasan gaban kungiyar dan kasar Faransa Alexandre Lacazette kwantiragi ba sai a karshen kakar bana duk da cewa ta san za ta iya rasa shi ba tare da samun ko kwabo ba a bazara. Atletico Madrid da AC Milan da Marseille da Newcastle duk suna zawarcin dan wasan. (Sun)

Pedri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pedri

Bayern Munich na son siyan dan wasan Barcelona Pedri, mai shekara 18.

Barcelonar za ta iya dakatar da kwantaragin Samuel Umtiti. Dan wasan bayan na Faransa, mai shekara 28, ya kasa amincewa da rage albashinsa na fam 208,000 a duk mako, sakamakon matsalar kudi da kungiyar ke fuskanta. (Sport in Spanish)

West Ham na kokarin daukar dan wasan Sparta Prague da Jamhuriyar Czech Adam Hlozek, mai shekara 19. (Footballer Inside)

Renato Sanches

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Renato Sanches

Dan wasan tsakiya na Lille Renato Sanches ya ce a shirye yake ya bar kulob din don fuskantar wani sabon kalubale. Arsenal da AC Milan na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan na Portugal mai shekara 24, wanda ya kusa kulla yarjejeniya da Barcelona a bazara. (L'Equipe, in French)

An ce kungiyoyi da dama na fakon Aleksandar Mitrovic na Fulham yana zawarcin a watan Janairu, inda Unai Emery na Villarreal ke cikin masu zawarcinsa. Dan wasan na Serbia, mai shekaru 27, ya zura kwallaye 21 a wasanni 18 a kakar wasa ta bana. (Mirrori

Bayern Munich na shirin bai wa dan wasan baya na Jamus Niklas Sule sabon kwantiragi, wanda zai yi watsi da fatan manyan kungiyoyin gasar Premier da suka yi niyyar siyan dan wasan mai shekaru 26 a kyauta. (TZ, in German