Abin da ƴan Saudiyya ke cewa kan cikar Sarki Salman shekara bakwai a kan mulki

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Saudiyya da dama sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta kan cikar Sarki Salman na ƙasar shekara bakwai a kan karagar mulki.

A ranar 8 ga watan Nuwamban 2021 da ya yi daidai da 3 ga watan Rabi'ul Akher shekara ta 1443 bayan hijira, Sarki Salman Bin Abdul'Aziz ke cika shekara bakwai a kan karagar mulkin Saudiyya.

Ƴan ƙasar sun ƙaddamar da maudu'ai da dama a Tuwita don taya sarkin nasu murnar wannan rana.

Ƴan Saudiyya sun yi ta tunawa da gagaruman ci gaban da ƙasar ta samu a dukkan fannonin rayuwa, da matakan da masarautar ta ɗauka don zama jagora a duniya, musamman bayan karɓar shugabancin ƙungiyar G20 ana tsaka da fama da annobar cutar korona.

Da dama na yi wa sarkin murna da godiya, musamman kan ƙoƙarin shawo kan yaɗuwar annobar cutar korona da ta kawo cikas ga yadda aka saba gudanar da ibadar Hajji da Umara.

A yau duniya na yi wa Saudiyya kallon wata kasa da ta jajirce ta ci annobar korona da yaƙi, ta hanyar ɗaukar tsauraran matakan daƙile cutar tun bayan ɓullar ta.

Daga samun labarin bullar cutar a ƙasar kawo yanzu, Saudiyya a karkashin Sarki Salman ta nuna da gaske take yi wurin magance ta, don tuni an yiwa kashi 70 cikin 100 riga-kafi.

An yi wa 'yan kasa da mazauna har ma da yan cirani da suka shigo ba bisa ƙa'ida ba riga-kafi, kuma a matakin duniya Saudiyya ta taka rawar gani wurin agazawa sauran kasashe yaƙar cutar.

A taron Majalisar Dinkin Duniya na 76 da aka yi a watan Satumban wannan shekara ta intanet, Sarki Salman ya bayyana cewa "Saudiyya ta taya duniya yaki da annobar korona da dala miliyan 800."

Ya kara da cewa "Saudiyya daula ce ta jinƙai da tausayin al'umma."

To amma ba wannan ce kadai gagarumar nasarar da za a ce Sarki Salman ya samu ba, lura da yadda ake samun haske kan shirin Saudiyya na 'Vision 2030', wani shiri na yi wa ƙasar garambawul da zai tabbatar da sauye-sauye ta fannin haɓakar tattalin arziki da kuma bai wa al'umma wasu damarmaki da a baya ba a ba su ba.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Me ƴan ƙasar ke cewa?

Ga abin da wasun su ke cewa a shafin Tuwita:

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

N @on_7 ya ce #ذكرى_البيعة_السابعة "Shekara bakwai ɗinnan ta ƙara wa ƙasarmu abubuwa da dama, inda aka cimma nasarori da dama a dukkan matakai na siyasa da tatatlin arziki da kuma zamantakewa."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

سند @i3sand ya ce "ba a yi wani sarki kamarsa ba.|

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

@Abrar42620477 ya ce: #ذكري_البيعه_السابعه "Muna alfahari da sarkinmu, babanmu kuma jagoranmu. Kana cikin zuciyar kowane ɗan Saudiyya."

Wannan layi ne

Sarki Salman ya zama sarkin Saudiyya

Sarkin mai shekara 85 ya zama sarki ne bayan rasuwar ɗan uwansa Sarki Abdullah ɗan Abdulaziz, wanda hakan ya ba shi damar zama mai kula da masallatai mafiya tsarki a duniya da ke biranen Makka da Madina.

Kafin ya zama Sarki, ya zama Yarima mai jiran gado, kuma a watan Nuwamban 2011 aka nada shi ministan tsaron Saudiyya.

Amma kafin wadannan mukamai, sai da ya shafe sama da shekara 50 a matsayin gwamnan Riyadh.

Shi ne ɗa na 25 ga Sarki Abdulaziz kuma ɗansa na shida cikin waɗanda suka yi sarauta bayan Sarki Faisal da Sarki Khalid da Sarki Fahd da kuma Sarki Abdullah.

Sauye-sauye a zamaninsa

Mata sun samu walwala sosai a mulkin Sarki Salman kamar yadda masu sharhi ke cewa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata sun samu walwala sosai a mulkin Sarki Salman kamar yadda masu sharhi ke cewa

Bugu da kari a karkashin mulkin Sarki Salman an samu sauye-sauye da ba a saba gani ba, wadanda suka janyo ce-ce-kuce ba a kasar kadai ba har ma a fadin duniya.

Tun hawan Sarki Salman bai ɓata lokaci ba wurin ƙaddamar da manyan ayyukan bunƙasa tattalin arziki da lafiya da ilimi da walwalar al'umma da sufuri da sadarwa da sauran ababen inganta rayuwar al'umma.

Kuma wadannan sauye-sauye sun shiga kowane lunga da saƙo na Saudiyya, a waje kuma Saudiyya ta samu nasarar bunkasar tattalin arziki da ya sa ta ja ragamar shugabancin kasashe mafiya karfin tattalin arziki na G20.

Sai dai mafi yawa ana ganin yarima mai jiran gado ne ke juya akalar masarautar kuma shi ke kawo sauye-sauyen da yawanci ake Allah-wadai da su.

Irin wadannan sauye-sauye dai sun haɗa da:

  • Ɗage haramcin shiga sinima ga maza da mata
  • Tarukan casu, wanda ko a watan Oktoban da ya gabata ma wani bidiyo da ya nuna mata da maza sanye da kayan ninkaya suna cashewa a bakin ruwan Jeddah ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar
  • Dage haramcin tuki ga mata
  • Bude gidan rawa a Saudiyya
  • Bikin kafa Saudiyya da ya kawo gwamutsa mata da maza
  • Kallon 'yan kokawa na Amurka
  • Tseren keken mata zalla da sauran su.
Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so

Wannan layi ne