Super Eagles ta je ta doke Cape Verde ranar Talata

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Super Eagles za ta karbi bakuncin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a wasa na uku a cikin rukuni ranar 9 ga watan Oktoba
An wallafa

Super Eagles ta je ta doke Cape Verde 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ranar Talata.

Cape Verde ce ta fara cin Najeria ta hannun Dylan Tavares a minti na 20 da fara tamaula, minti 10 tsakani Super Eagles ta farke ta hannun Victor Osimhen.

Sauran minti 14 a tashi daga fafatawar Najeriya ta kara na biyu, bayan da Kenny Rocha Santos ya ci gida.

Da wannan sakamakon Super Eagles tana mataki na daya a rukuni na uku da maki shida, bayan buga wasa biyu.

Ranar Juma'a 3 ga watan Satumba Najeriya ta yi nasara a kan Liberiya da ci 2-0 a wasan farko na cikin rukuni a jihar Legas.

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ce ta biyu mai maki hudu, bayan da ta je ta ci Liberiya 1-0 ranar Litinin 6 ga watan Satumba.

Cape Verde ce ta uku a teburi na ukun da maki daya, sai kuma Liberiya ta hudu wadda ba ta da maki ko daya.

Super Eagles za ta karbi bakuncin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a wasa na uku a cikin rukuni ranar 9 ga watan Oktoba, a ranar kuma Liberiya ta karbi bakuncin Cape Verde.

Qatar ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya da za a yi a 2022.