Premier League: A karon farko bayan shekara 24 Brenford ta ɗauki fansa kan Arsenal

Wannan ne karon farko da Brentford ta zo gasar Premier a cikin shekaru 74

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da Brentford ta zo gasar Premier a cikin shekaru 74
An wallafa

Brentford ta yi shagalin dawowa gasar Premier bayan shekara 74 da doke Arsenal a filinta na Community Stadium da ke yammacin London.

Rabon da ƙungiyoyin su hadu da juna tun shekarar 1997, a wani wasan hamayya da Arsenal da doke Brentford 5-0.

Ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da 'ƙudan zuma' ta harbi Arsenal har sau biyu a wasan farko na gasar Premier ta bana, inda aka tashi 2-0.

Ba wannan ba kawai, abune a zahiri Brentford ta matse Arsenal daga farkon wasan har ƙarshe.

Kuma a minit na 22 ne ɗan wasan gefe Sergi Canos yaci kwallon farko bayan ya shigo daga gefen dama.

Sai kuma a minti na 73 ne Norgaad yaci ƙwallo ta biyu da ka, abinda ya sa wasan ya tashi 2-0.

Arsenal ta sha kashin ne duk da fara wasan da ɗan wasan bayan da ta saya daga Brighton wato Ben White kan fam miliyan 50.

Sai dai kuma ƴan wasan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang da Alexander Lacazatte ba su buga wasan ba saboda jinyar rauni da suke yi.

A gobe ne za a cigaba da wasannin na makon farko, inda Manchester United za ta kece raini da Leeds United, inda ranar Lahadi za a buga wasa mafi zafi na makon tsakanin masu rike da kofi wato Manchester City da kuma Tottenham.