Kwangilar layin dogo daga Kano zuwa Maraɗi ta yi tsada – Masana

..

Asalin hoton, Nigeria Presidency

An wallafa

Gwamnatin Nijeriya ta sa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfani mai suna Mota-Engil Group don gudanar da aikin shimfiɗa babban layin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke Jamhuiyar Nijar.

Aikin wanda gwamnati ta ce za a kammala nan da shekara ta 2024, zai lashe kuɗi dala biliyan 1. da miliyan 959.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ambato ministan sufurin ƙasar, Rotimi Amechi a cikin wata sanarwa na cewa aikin na da nufin haɗe ɗaukacin Nijeriya da layin dogo.

Ambasada Yusuf Tuggar jakadan Nijeriya ne a Jamus, ƙasar da za a samo kuɗin gudanar da aikin, kuma yana ɗaya daga cikin jami'an gwamnatin Nijeriya da suka shaida sa hannu kan yarjejeniyar.

Ya shaida wa BBC cewa "akwai bankin gwamnati na ayyuka KFW da zai haɗo kuɗaɗen da za a yi aikin, zai tafi daga Kano zuwa Maradi sannan daga Kano zuwa Dutse a jihar Jigawa".

Ya ce gudanar da aikin zai samar da damarmaki da dama ga ƙasar ta fuskoki daban-daban.

A cewarsa, "mafi yawan kuɗaɗen bashi ne sai dai a ciki ba za a rasa gudummawar da za a bayar ba ta koyon sana'a, tun da sai an horar da ma'aikata ayyuka".

"Cikin shekara 15 za a kammala biyan basukan kuma kamfanin ya ba da tabbacin kammala aikin cikin shekara uku saboda kamfani ne da ya ƙware a irin wannan aikin". in ji Tuggar.

Sai dai kuma masana a ɓangaren tattalin arziki irinsu Dakta Shamsuddeen Muhammad suna ganin duk da ɗumbin ƙaruwar da za a samu daga aiwatar da wannan aiki, akwai rashin fa'idarsa.

"Kudin da aka ware kamar ya yi yawa sosai, kamar kwangilar ta yi tsada" sannan kuma a cewarsa, akwai abin damuwa a yadda gwamnati take ciwo bashi yana mai cewa a yanzu, bashin da ake bin Najeriyar ya haura kashi 10 cikin 100 na gaba ɗaya tattalin arzikin ƙasar.

Tun cikin watan Satumba ne gwamnati ta sanar da ƙudirinta na wannan aikin, sai dai lamarin ya tayar da ƙura inda mutane da dama suka riƙa sukar batun.