Yadda aka bankado badakalar 'yar tsohon shugaban Algeriya

An wallafa

An yanke wa wata 'yar kasuwa da aka yi amannar diyar da tsohon Shugaban Algeriya, Abdelaziz Bouteflika, da ya haifa a asirce ce hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari saboda halatta kudaden haram da kuma barnatar da kudaden jama'a.

Nachinachi Zoulikha, wacce ake kira da Mme Maya, ta musanta cewa ba ta taba gaya wa kowa cewa ita 'yar Mista Bouteflika ba ce.

Kafofin watsa labarai na cikin gida a kasar sun ruwaito cewa an yi wa Misis Zoulikha alfarma ta musamman don sanya hannun jari da kuma kwasar kazamar riba albarkacin mahaifinta.

Jita - jita game da alakarta da shugaban ta yi karfi ne lokacin da ta nemi gwamnan birnin Oran da ya taimaka wajen kafa mata wani sabon babban kanti.

Gwamnan aboki ne, ga dan uwan shugaba Bouteflika da ake kira Sa'id.

Sai dai Sa'id din ya musanta cewa yana da alaka da batun, tuni ma ya shigar da kara kotu don neman a wanke shi.

Lokacin da aka cafke ta a shekarar 2019, masu binciken sun kama ta da tsabar kudi kusan Euro miliyan daya, baya ga dalar Amurka dubu 30 da gwala-gwalai da ta boye a bangon gidanta.

Kotun da ke Algiers babban birnin kasar, ta umarci Zoulikha da ta biya tarar dinari na Algeriya miliyan shida, tare da kwace dukkanin kadarorin da ta mallaka.

'Ya'yanta mata biyu Imen da Farah suma an daure su tsawon shekaru biyar kowannensu tare da cin tarar dinari na Algeria miliyan uku.