Tsoffin firai ministocin Algeria za su je zaman gidan yari

An wallafa

Wata kotu a Algeria ta yanke wa tsoffin firai ministocin kasar hukuncin dauri bayan samun su da aikata laifin zamba.

Wannan shi ne karon farko da ake daure wani tsohon firai minista tun bayan samun 'yancin kan kasar daga Faransa a 1962.

Kotun ta samu tsoffin firai ministocin kasar da suka hada da Ahmed Ouyahia da kuma Abdelmalek Sellal da laifin satar kudaden gwamnati a badakalar wani kamfanin kera motoci.

Ahmed Ouyahia zai yi shekara 15, shi kuma Abdelmalek Sellal shekara 12 a gidan yari.

Kotun ta kuma yanke wa wani minista mai ci daurin shekarar ashirin.

Alkalin ya kuma tsare da bayar da umunin tsare Abdesalem Bouchoureb a duk inda ya ke, bayan rahotonnin da ke cewa yana kasashen ketare.

Ta kuma daure wasu tsoffin jami'an gwamnati shida a gidan kaso kan cin hanci da rashawa.

Tsoffin fira ministocin na daga cikin mutum 19 da ake bincike a badakalar almundahana bayan an tilasta wa Firai minitan Abdelaziz Bouteflika sauka daga mulki.

Sai dai lauya mai kare wadanda ake karar ya kaurece wa zaman kotun bisa zargin bita da kullin siyasa.

Wadanda aka yanke wa hukuncin da na kwanaki 10 su daukaka kara.

Hukuncin kotun na zuwa ne kwana biyu kafin zaben magajin Bouteflika.

Masu fafutuka sun shafe makonni suna gudanar da zanga-zanga a kan tituna don neman dakatar da zaben mai tahowa.