Hadarin jirgi: Mutum 5 sun mutu a taho mu gaman jiragen sama a Faransa

Asalin hoton, Getty Images
Wasu jiragen sama biyu a Faransa sun yi taho mugama a sararin samaniya, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane biyar.
Hadarin ya faru ne a yankin kudu maso gabashin Faransar da yammacin Asabar.
An killace yankin da jiragen suka fadi bayan taho mu gamar da suka yi, yayin da yan kwana kwana ke ci gaba da aikin kashe wuta.
Wani ganau ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa karamin jirgin mai dauke da mutane biyu kacal ne ya fara kamawa da wuta, bayan da ya fada kan wayar lantarki.
Haka ma babban jirgin kirar Diamond DA40 ya fadi ne da tazarar mita 100 tsakanin su dauke da yan yawon bude ido uku.

Asalin hoton, Getty Images
A yanzu hukumomi na kokarin tantance bayanan mutanen da hadarin ya rutsa da su.
Kuma tuni an kaddamar da binciken gano musabbabin afkuwar hadarin.
Ba kasafai a ke samun hadarin jirage ba ta hanyar taho mu gama, to amma ko a shekarar 1998 an taba samun irin wannan hadari a yankin Quiberon Bay da ke Faransar, da ya yi sanadin mutuwar mutun 15.









