Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Duka masu cutar korona a Zamfara sun warke'
Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce yanzu babu wanda ke dauke da cutar korona a jihar, don haka ma sun sallami mutanen da suka yi saura a cibiyar killace mutane da ke jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Yahaya Muhammad Kanoma ya shaida wa BBC cewa mutum takwas ne kawai suka yi saura a jihar kuma ya zuwa yanzu duk sun sallame su.
Dakta Yahaya ya bayyana cewa tun kafin cutar korona ta ɓulla jihar, tuni gwamnatin Zamfara ta tanadi kayayyakin na'urarorin taimaka wa numfashi da sauran na'urori na yaƙi da cutar
Mutum biyar ne cutar ta kashe a jihar ta Zamfara tun bayan bullarta.
Kamar yadda ƙididdigar hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa NCDC ta bayyana, mutum 76 ne kacal aka tabbatar da sun kamu da cutar ta korona a jihar.
Sai dai duk da gwamnatin jihar ta tabbatar da babu mai cutar ta korona a jihar, babu tabbaci kan ko yaushe za a buɗe makarantu da sauran wuraren kasuwanci kamar yadda suke kafin bullar annobar.