Masu cutar korona 'suna tserewa a Zamfara'

An wallafa

Masu cutar korona a jihar Zamfara da ke Najeriya suna tserewa daga cibiyar killace masu dauke da cutar saboda rashin kyawunta.

Wasu da aka killace a cibiyar sun shaida wa BBC cewa rashin kyawun wurin musamman rashin makewayi ya sa ba sa iya sukuni.

''Makewayin mu guda don haka idan mutum yana cikin matsuwa sai dai ya samu leda ko idan dare ya yi ya fita ta taga ya je ya kau da wannan matsalar''

A cewarsu, da farko an kai su wani wuri a Damba da ke wajen Gusau, babban birnin jihar amma ganin rashin kyawunsa ya sa an dauke su zuwa asibitin kwararru na Ahmed Sani Yariman Bakura.

Sai dai da alama an yi gudun gara an tada zago saboda wani wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa BBC cewa likitoci ba sa taba su, suna cewa babu kayan kariya.

''Babu batun ruwa sai wanda ake kawo wa a jarkoki, kullum kuma sai sun yi korafi cewa babu ruwan ko na korawa a bundaki babu''

Marasa lafiyar sun ce akwai sakaci na ma'aikatan lafiyar asibiti, an gaggara tabbatar da sakamakon gwajin da aka yi musu na cutar inda aka bukaci su sake mika kansu domin a kara gwada su.

Kakakin majalisar Jihar Hon. Nasiri Mu'azu Magarya wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da wannan annobar a Zamfara ya amsa cewa akwai matsala, amma ya ce suna iya kokari domin daukar mataki a kan batun.

Hukumomin Jihar dai ba su musanta wadanan korafe-korafe ba, sai dai sun nuna kawai karanci kayayyaki da ake bukata wurin bai wa marasa lafiyar kulawa.

Wannan ba shi ne karon farko da ake samun irin wadanan korafe-korafe kan rashin kyawun cibiyar masu dauke da wannan cuta a yankin arewacin Najeriya ba.

Ko a cikin makon da ya gabata sai da wadanda aka killace a wata cibiya da ke Gombe suka gudanar da zanga-zanga saboda rashin basu kyakyawan kulawa.