Coronavirus: Masu dauke da cutar sun haura miliyan 4 a duniya

Kwararu sun yi gargadi kan sake yaduwar corona sakamakon sakaci da rashin jin gargadi a wasu kasashe da dama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwararu sun yi gargadi kan sake yaduwar corona sakamakon sakaci da rashin jin gargadi a wasu kasashe da dama
An wallafa

Sama da mutum miliyan 4 aka rawaito na dauke da cutar korona yanzu haka a fadin duniya.

Alkaluman da Jami'ar John Hopkins ta fitar sun ce mamata sun karu zuwa 277,000 sakamakon annobar.

Amurka ce kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda kashi 1 bisa 4 na adadin masu dauke da cutar da kashi 1 bisa 3 na mamata 'yan kasar ne.

Kwararu sun yi gargadi sake samun karuwar wadanda za su kamu da cutar, yayinda kasashen ke fuskantar karancin gwaje-gwaje da bayanai.

An samu ragin rasa rayuka a wasu kasashen, ciki akwai Spaniya, sai dai akwai fargabar da ke nuna sassauta dokar kulle ka iya sake fantsama annobar a ''karo na biyu''.

Bugu da kari, gwamnatoci na rungumar matakan farfado da tattalin arziki, yayinda annobar ta yi illa ga kasuwanci a duniya da kassara duk wasu hada-hada.

A wasu daga cikin manyan ci gaba da aka samu a baya-bayanan:

  • Gwammnatin Burtaniya za ta cigaba da daukan matakai cikin ''yanayi na takatsantsan'' yayinda take duba yiwuwar sassauta dokar kulle, a cewar sakataren harkokin sufurin kasar.
  • Shugaban China ya nuna damuwa kan barazanar coronavirus a Korea ta Arewa tare da mika tayin bada taimako.
  • Hamshakin attajiri mai kamfanin Telsa, Elon Musk ya ce zai mayar da hedikwatar kera motocinsa zuwa California saboda matakan hana zirga-zirga a tsakanin jihohi.
  • Jami'an lafiya a Ghana sun ce sama da ma'aikata 500 da ke aiki a wata masana'anta sun kamu da cutar korona, yayinda adadin masu kamuwa da cutar ya karu da kashi 30 cikin 100 a ranar guda - kwana guda da sanar da cewa cutar ta kai kololuwa.
Karin bayani kan coronavirus

A wannan makon, An dage dokar kulle a Italiya, wacce ta taba zama cibiyar annobar a duniya. 'Yan Italiya sun samu damar fitowa motsa jiki da ziyarta 'yan uwa a yankunansu.

Faransa sama da wata guda yanzu ana samun raguwar masu mutuwa sakamakon wannan cuta, inda mutum 80 kawai suka mutu a cikin sa'o'i 24. Mahukunta na shirin sassauta dokar hana fita daga Litinin, kamar yadda makociyarta Spaniya ta yi.

A kasashen irinsu Afirka ta Kudu kuwa dokar hana fita na ci gaba da aiki, duk da kiraye-kirayen da 'yan adawa ke yi na a kawo karshen dokar.

A Korea ta Kudu, an sake daukan sabbin matakai a kan shagunan sayar da barasa da gidan rawa, bayan sake samun rahotan yaduwar cutar a irin wadanan wurare a Seoul.

Shugabannin kasashe da dama na cigaba da bayyana fatansu na shawo kan annoba da alfannu dokar kulle.

A Belarus, dubban sojoji sun gudanar da faretin bikin cika shekara 75 da nasara a yakin duniya na biyu, bayan Shugaba Alexander Lukashenko ya yi watsi da bukatar daukan matakai masu tsauri kan annobar.

Mujallar kiwon lafiya ta Lancet a Burtaniya ta wallafa wata makala kan shugaban Brazil Jair Bolsonaro, wanda ta bayyana a matsayin babban barazana ga kasar sa kan gaza shawo yaduwar annobar korona. Brazil a yanzu ita ce mai yawan masu dauke da wannan cuta a kasashen Latin Amurka, sai dai shugabanta har yanzu bai yadda akwai cutar ba, sanna ya sha rigima da gwamnoni kan daukan matakan hana zirga-zirga.

Karin bayani kan coronavirus