Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Yan Najeriya kimanin 1,000 sun kamu a kwana 4
Alkaluman hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya na ranar Alhamis sun nuna cewa kusan karin mutum 400 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a kasar, abin da ya sa yawan masu cutar a daukacin Najeriya ya zarce 3,500.
A cewar alkaluman a jihohin Najeriya uku kawai wato Lagos da kano da kuma Jigawa, an samu kusan mutum 300 da suka sake kamuwa da annobar tashi guda.
Jihar Legas, ce a kan gaba da mutum 183 wadanda korona ta shafa, sai jihar Kano mai mutum 55, yayin da makwabciyarta Jigawa ta samu sabbin kamuwa da cutar 44.
Wadannan ne alkaluma mafi yawa na mutanen da aka gano cutar ta harba da hukumomin Najeriya suka taba fitarwa cikin kwana guda tun bayan bullar annobar ranar 27 ga watan Fabrairu.
Yawan mutanen da aka sanar sun sake kamuwa da cutar a ranar Alhamis wato 381, sun sa a cikin kwana hudu kacal an samu karuwar kusan mutum dubu na masu korona.
Bayanan masu cutar korona da hukumar NCDC ta fitar na ranar Lahadi sun nuna cewa karin mutum 170 da aka samu sun harbu da annobar ya sa adadin masu korona ya kai 2,558.
Hukumar ta shafe tsawon kwana 70 kafin samun yawan masu cutar korona sama da 2,500 a fadin Najeriya.
Sai dai, daga washe gari ranar Litinin zuwa Alhamis 7 ga watan Mayu, mutum 968 ne aka gano sun sake kamuwa a fadin kasar. Karin kimanin kashi 27 cikin 100 a kasa da mako daya.
A cikin adadin, har yanzu a jihar Lagos ne aka samu alkaluma mafi yawa na sabbin kamuwa da korona a cikin kwana hudu da 384. Kafin nan yawan masu cutar ya zuwa ranar Lahadi 1,107 a Lagos.
Haka zalika, daga ranar Litinin zuwa Alhamis, an sake gano masu cutar korona mutum 140, karin kimanin kashi 30 cikin 100 a kwana hudu.
Fiye da kashi hamsin cikin 100 na mutanen da suka sake kamuwa da cutar korona cikin kwana hudun nan a Najeriya, sun fito ne daga jihohin Lagos da Kano, nan kuma annobar ta fi kamari a kasar.
Jigawa na daga cikin jihohin da aka samu hauhawar alkaluman masu cutar a 'yan kwanakin nan, don kuwa a ranar Lahadi mutum bakwai ne kacal aka tabbatar suna da korona a jihar.
Sai dai yanzu sun karu zuwa mutum 83. Haka ma Katsina inda cikin kwana hudu aka samu karin mutum 60 da aka tabbatar sun sake kamuwa.
A Zamfara ma an fuskanci gagarumin kari na masu cutar a cikin kwana hudu, don kuwa zuwa ranar Lahadi, bayanan NCDC sun nuna mutum 12 ke da cutar, kafin su karu zuwa 65 a ranar Alhamis.
Bauchi ma ta samu karin mutum 31 da suka sake kamuwa a kwana hudu, yanzu haka yawan masu korona a jihar sun kai mutum 102.
To, ko me ya janyo saurin karuwar alkaluman masu fama da korona a cikin wannan mako? Hukumomin Najeriya dai sun ce sun kara cibiyoyin gwada mutanen da ake zargi suna da korona.
A jihar Kano kawai, kimanin cibiyoyin gwaji uku ne yanzu ke aiki, inda suke karbar samfuran danshin makogwaro ba kawai daga Kano ba, har ma daga jihohi makwabtanta.
Haka zalika, hukumar NCDC ta bayyana a cikin rahoton da takan fitar game da yaki da annobar cewa ya zuwa ranar Alhamis ta cimma adadin gwada samfur 1,000 a kullum.