NFF za ta dunga taimakon mahaifiyar Yekini da ta Okwaraji

An wallafa

Hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF ta tsara yadda za ta dunga taimakon mahaifiyar Rashidi Yekini da ta Sam Okwaraji kowanne wata.

NFF za ta dunga bayar da naira 30,000 ga mahaifiyar tsoffin 'yan wasan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya biyu da tuni suka mutu.

Hakan ya biyo bayan da Ministan wasanni da matasa na Najeriya, Sunday Dare ya bai wa iyayen gudunmawa ya kuma ce zai ci gaba da taimaka musu.

Haka kuma NFF za ta duba halin da duk wasu iyalan tsoffin 'yan kwallon Najeria, wadanda suka mutu ke ciki, domin zakulo hanyoyin da za a taimaka musu a kowanne lokaci.

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Nigeria, Shehu Dikko ya ce ba wannan ne karon farko da suke taimakon iyalai da kuma tsoffin 'yan wasan da suka buga wa Najeriya kwallo ba.

Yekini ya fara yi wa Super Eagles wasa a 1984 ya kuma ci mata kwallo 37 a wasa 58 har yanzu shi ne kan gaba a zura kwallo a raga a kasar.

Shi ne ya fara ci wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya a 1994 a karawar da Super Eagles ta doke Bulgaria 3-0, kuma har yanzu ana tuna murnar da ya yi, inda ya shiga raga ya daga ta da hannu biyu yana kuka.

Yana daga cikin 'yan kwallon da suka ci wa Super Eagles kofin nahiyar Afirka a 1994 a Tunisia, kuma ya wakilci kasar a gasar Olympic a Seoul a 1988.

Yekini ya mutu a garin Ibada ranar 4 ga watan Mayun 2012 yana da shekara 48.

Shi kuwa Sam Okwaraji ya fara yi wa Super Eagles tamaula a 1988 lokacin da ake kiranta da Green Eagles a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

A lokacin ya ci wa Najeria kwallo kuma ita ce aka zura a raga cikin kankanin lokaci a tarihi a fafatawa da Kamaru wato Indomitable Lions.

Okwaraji ya fadi ya mutu a fili a lokacin da yake buga wa Najeriya wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a 1990 a fafatawa da Angola a Legas yana da shekara 25.

Dan wasan ya buga wa Najeriya wasa takwas ya kuma ci mata kwallo daya tal.