Covid-19: Nan da mako 2 za a aika wa Amurkawa tallafin kudi

President Trump at the White House

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Shugaba Trump ya sa hannu kan dokar kunshin kudi mafi girma a tarihin Amurka, don zaburas da jama'a da kuma rage radadin annobar koronabairus kan tattalin arzikin kasar.

Tun da farko sai da kudurin dokar na dala tirliyan biyu ya samu amincewar Majalisar wakilan Amurka, inda duka 'yan jam'iyyar Republican da takwarorinsu na Dimokrat suka ce ya zama tilas don tallafa wa Amurkawa magidanta da 'yan kasuwa.

Miliyoyin Amurkawa ne tuni suka rasa ayyukansu sakamakon wannan annoba ta koronabairus.

Amurkawa kimanin miliyan 3 da dubu 300 ne ala tilas suka yi rijista don samun tallafin da ake bai wa marasa aikin yi saboda annobar,

Shugaba Trump ya ce kunshin tallafin kudin zai kawo saukin da ake bukata cikin gaggawa ga iyalan kasar da ma'aikata da kuma harkokin kasuwanci.

Ana fatan za a aika cekin kudi ga Amurkawan a cikin mako biyu.

Duk Ba'amurken da ke daukar albashi kasa da dala 75,000 a shekara. zai samu agajin dala 1,200 zuwet.

Yayin da asibtoci a fadin kasar ke kokarin biyan bukatun adadin marasa lafiyan da ke k'aruwa, Shugaba Trump ya ce za a yi amfani da biliyoyin daloli wajen sayo kayan bukatun asibiti a karkashin dokar samar da kayayyakin tsaro.

Dokar dai ta bai wa shugaban kasar ikon tilasta wa masana'antun 'yan kasuwa samar da kayayyakin da ake bukata don tsaron kasa.

Ya ce ana bukatar hakan don tilasta kamfanin kera motoci na Geneal Motors ya sarrafa na'urorin tallafawa yin numfashi, wadanda gwamnatin tarayya za ta raba.

Mista Trump ya ce yana da kyakkyawan fatan cewa nan gaba kadan asibitocin da ke bukatar kayan aikin za su same su.

New York ya ci gaba da kasancewa matattarar wannan annoba a Amurka, ko da yake sauran birane ciki har da Chicago da New Orleans da Detroit su ma sun samu habakar mutanen da ke neman kulawar likitoci saboda kwayar cutar