An dakatar da zuwa aikin gwamnati a jihar Lagos na tsawon kwana 14

Gwamna Babajide Sanwon-Olu ya ce cutar ta coronavirus ba abin wasa ba ne

Asalin hoton, Lagos State Government

Bayanan hoto, Gwamna Babajide Sanwon-Olu ya ce cutar ta coronavirus ba abin wasa ba ne
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta umarci ma'aikata da ke mataki na daya zuwa na sha biyu da ke a aiki a hukumomin gwamnatin jihar su zauna a gida tsawon mako biyu domin kace wa kamuwa da coronavirus.

Gwamna Babajide Samwo-Olu na jihar ne ya bayana hakan ranar Lahadi a jawabin da ya yi wa jama'ar jihar.

Ya ce daukar matakin ya zama wajibi idan aka yi la'akari da yadda cutar take kara yaduwa a duniya.

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya ta ce ya zuwa yanzu mutum 35 ne suka kamu da annobar coronavirus a Najeriya, kuma 27 daga cikinsu a jhar Lagos suke.

Gwamna Samwo-Olu ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu a jihar su yi amfani da wannan dama domin takaita yawan ma'aikatansu da za su rika zuwa aiki.

Kazalika gwamnan ya yi kira ga mutanen da su ka dawo daga kasashen waje su killace kansu na tsawon mako biyu domin sanin ko sun kamu da cutar ko basu kamu da ita ba.

Ko da yake ba a hana mutane fitowa a birnin na Lagos ba, amma gwamnan ya bukace su su rika samar da tazara a tsakaninsu domin gudun kar su harbu da kwayar cutar ta coronavirus.

Jihar Legas dai na da al'umma kimanin miliyan ashirin kana kuma ta kasance wata jiha da kusan al'ummarta sai je kasuwa domin saya ko a sayarwa .

Wannan umarni dai bai hada da hukumomin kula da lafiya da jami'in kashe gobara da kuma da sauran hukumomi da ke ayyukan gaggawa ba.

'Ma'aikatan Kaduna za su kwana 30 a gida'

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A bangare guda, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar ranar Litinin cewa ma'aikatanta da ke matakin albashi 12 zuwa kasa za su zauna a gida tsawon kwana 30 domin kauce wa kamuwa da coronavirus.

A sakon da gwamnati a wallafa a shafinta na Twitter, ta kara da cewa daga ranar Talata, masu sayar da abinci da magunguna kawai za a bari su bude shaguna a kasuwannin jihar.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya ce gwamnati ta haramta tarukan jama'a kuma za ta tabbatar an yi aki da dokarta.