Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsaro: Shugaba Buhari ba zai yi murabus ba - Lai Mohammed
Gwamnatin Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi murabus ba duk kuwa da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta a yanzu.
Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, babban birnin kasar.
Ministan ya kuma mayar da martani kan kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar ke yi na cewa shugaban ya sauka daga kan kujerarsa saboda gazawarsa a fannin tsaro.
A cewar ministan, Buhari ya samu lamincewar jama'a kan tafiyar da harkokin kasar har zuwa karshen wa'adin mulkinsa a Mayun 2023.
Ministan wanda ya tabbatar da matsalolin tsaron, ya bayyana cewa gwamnati tana bakin kokari don magance matsalar.
Ya kuma shawarci masu fada a ji da ke kasar musamman malaman addini da 'yan siyasa, da su rika sanin kalaman da za su furta domin kaucewa fadin abubuwan da za su haifar da rarrabuwar kai a tsakanin 'yan kasar.
Ministan ya yi tsokaci kan rahoton Kungiyar Amnesty International kan zargin sojojin kasar da kone wasu kauyuka tare da tilasta wa mutane barin muhallansu.
"Na san cewa rundunar sojin ta mayar da martani game da zarge-zargen," a cewarsa.
Ya nemi Amnesty da ta daina bai wa 'yan ta'adda mafaka kan yadda suke alakanta ta'addancin da suke kai wa ga sojojin kasar.
"Sojojinmu da suke tsaron kasa suna baibaye da dokoki wajen gudanar da ayyukansu.
"Na san gwamnati tana daukar zarge-zargen take hakkokin bil adama da ake yi wa sojoji da muhimmanci, kuma an gudanar da bincike sannan za a hukunta masu laifi," in ji Lai Mohammed.
Game da yada labaran kanzon kurege kuwa, Lai Muhammed ya ce wannan dabi'a ta yada labaran karya ta zama wani makami na haifar da tashin hankali a kasar.
"Kuma masu yin abin ba su da alamar yin nadama," kamar yadda ministan ya fada wa 'yan jarida.
Ya kuma ba da misalai kan labaran karyar da aka rika yadawa "babban misali shi ne wani hoton bidiyo na sama da matasa 400 da ake zargin 'yan Boko Haram ne da aka kama su a Abia a 2014."
"Makwanni biyu da suka gabata, an sake dawo da hoton bidiyon inda ake yada shi domin kawai a tayar da hankali."
"Wasu misalan na baya-bayan nan su ne Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya Birtaniya inda zai shafe kwanaki 20 sannan ya wuce Saudiyya da kuma Austria."
Sai dai tuni fadar shugaban kasar ta musanta wannan labarin.
Ministan ya kuma ce "muna kokarin tsaftace kafofin sada zumunta, muna aiki da masu ruwa da tsaki, kuma ranar 2 ga Maris din 2020 za mu kaddamar da kwamitin masu ruwa da tsaki kan haka."