Ana hasashen bullar Coronavirus a Ivory Coast

Asalin hoton, EPA
Hukumomin lafiya a Ivory Coast na hasashen bullar cutar Coronavirus.
Ma'aikatar lafiya a kasar ta sanar da cewa wata daliba da ba ta bayyana sunanta ba ta dawo daga Chana dauke da wasu alamun cutar da suka hada da mura.
A yanzu ana kan binciken abunda ke damunta don tabbatar da hasashen.
Idan har a ka tabbatar cewa tana dauke da kwayar cutar Coronavirus, zai zama karon farko da a ka samu bullar cutar a Afrika.
A halin yanzu matar mai shekaru 34 tana killace a wata cibiya inda a ke gudanar da binciken.
Ta na zaune ne a Chana tsawon shekara biyar ta kuma zo ganin gida ne, kamar yadda sanarwar da ma'aikatar lafiyar ta fitar.

Tun bayan bullar cutar, kasashen Afrika suka kara tsaurara binciken lafiyar matafiya musamman wadanda suke shigowa nahiyar daga Chana.
Ko a Chanar hukumomi sun haramta gudanar da taruka, a daidai lokacin da suka sanar da mutuwar mutane 80, kuma wasu sama da 3,000 sun kamu.
Yawancin wadanda suka mutu a birnin Wuhan ne, inda cutar ta fara bulla, yayin da Henan da Shanghai nan ma cutar ke kara yaduwa.
Hukumomi a birnin Beijing da Shantou a gundumar Guangdong sun aike da sakon kar ta kwana na wayar salula, tare da umartar jama'a idan za su gaisa ba sai sun sha hannu ba.









