Gobara ta tashi a kasuwar katako da ke Mushin a Legas

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta tabbatar da afkuwar wata gobara a kasuwar katako ta Amu da ke unguwar Mushin a jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Gobarar dai ta fara ne a ranar Asabar da misalin karfe 2 na dare kafin wayewar gari.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa na hukumar Nosa Okunbor ya shaida wa BBC cewa tun bayan da suka samu labarin gobarar, jami'ansu suka garzaya wurin domin kashe wutar.

Mista Okunbor dai ya bayyana cewa har yanzu ba su da masaniya kan takamaimai abin da ya jawo gobarar.

A wani bangaren kuma, tuni jama'a da dama a kafafen sada zumunta musamman mazauna Legas din suka fara mayar da martani kan gobarar inda suke yin kira ga gwamnati da ta yi wani abu domin akasari nan iyalensu ke samun na kunu.

Wannan mai suna Adufe a shafin Twitter cewa take yi kusan duka 'yan gidansu a kasuwar suke sana'a, ta ce mahaifinta yana da shaguna uku, kakarta ma na da shaguna, gwaggoninta biyu na da shaguna da dakunan ajiyar kaya, ta koka da cewa duka shagunan gwaggoninta sun kone cikin dare daya.

Ita ma Oluwatoyin a shafinta na Twitter ta koka da cewa a kasuwar ne kusan duka 'yan gidansu ke samun kudi, ta ce ji takaicin ganin duka kayansu sun kone kuma ba a kawo agaji ba sai bayan awa hudu.

Ko a kwanakin baya a jihar ta Legas sai dai mutum uku suka mutu sakamakon wani bututun mai na babban kamfanin man fetur na kasar, NNPC, da ya kama da wuta.

Kafin nan ma an samu rushewar wani gini mai hawa biyu da ke titin Ago Palace a jihar ta Legas.