Macen da ta fi kudi a Afirka ta mallaki dukiya ta haramtacciyar hanya - Bincike

Asalin hoton, Google
Wani binciken kwakwaf da sashen BBC Panorama ya gudanar ya gano cewa macen da ta fi kowa ce mace kudi a nahiyar Afirka ta samu kudin ne ta haramtacciyar hanya.
Isabel Dos Santos ta samu makudan kudade ta hanyar gudanar da haramtaccen kasuwanci da kamfanonin da ke hulda da gwamnatin mahaifinta Shugaba Dos Santos.
Wadannan kamfanoni na huldar kwangiloli a lokacin da mahaifin nata shugaban Angola Dos Santos yake mulki.
An samu tsegumin fitar takardu sama da 700,000 na kasuwancinta daga masu kwarmata bayanai na nahiyar Afirka, kuma sun bai wa kungiyar kwararrun 'yan jarida masu binciken kwakwaf na kasa-da-kasa.

Takardun sun nuna cewa akwai shaidun da ke nuna cewa wasu al'amuran kasuwancin da take gudanarwa akwai alamun cin hanci da rashawa.
An gano cewa mahaifinta da ya shafe shekara 38 yana mulkin Angola yana bayar da kwangiloli ga kamfanoni da sharadin ba da kamasho ga 'ya'yansa, kuma Isabel na cikinsu.
Haka ma an gano cewa kamfanin mai na kasar Sonagol, ya bai wa 'yar tsohon shugaban wata kwangila mai tsoka sosai.

Kuma da kudin kwangilar ne ta sayi kaso 15 na hannun jari a wani kamfanin makamashi na kasar Focugal.
Wannan kwangila ta samar mata da kaso uku bisa hudu na Yuro biliyan daya.
Yanzu haka Isabel na zaune ne a Burtaniya, kuma ta mallaki manyan gidaje masu tsada a kwaryar birnin Landan, tana kuma kasuwanci da kamfanonin man fetur da deman da kuma na sadarwa.
To sai dai Isabel ta musanta sakamakon wannan bincike, inda ta danganta shi da wani bita da kullin siyasa daga gwamnatin Angola.
A halin yanzu Isabel Dos Santos na fuskantar bincike daga hukumomi a Angola kan zargin cin hanci da rashawa, an kuma rike duk wata kaddara da ta mallaka a kasar yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken.
A cewar Andrew Feinstein na mujallar Corruption Watch, wannan balli ya nuna irin yadda Isabel Dos Santos ke cin karenta ba babbaka da kudin talakawa.
Ana ganin cewa dadewar mahaifinta kan karagar mulki na tsawon shekara 38 ne ya ba ta damar gudanar da wadannan huldodi yadda take so.
To amma duk da haka, wasu 'yan Angola na zargin shugaba mai ci Joao Lourenço da kokarin cimma burinsa na siyasa ta hanyar binciken iyalin wanda ya gada.












