Shahararren bikin 'yan matanci a Japan

An wallafa

Japan ta ayyana ranar 'yan matanci a kasar, inda akan bai wa dalibai da ma'aikata hutu dan taya 'yan matan da suka kai shekara 20 murna, kuma ana gudanar da bikin ne a hukumance dan yi musu maraba da kai wa wannan lokacin.

Ana gudanar da wannan biki ne a ranar Litinin ta biyu a watan Janairun kowacce shekara, 'yan matan da suka cika shekara 20 a shekarar da ta gabata ake sanya wa a bikin da ake yi a wani babban dakin taro da ke birnin Tokyo da sauran wurare a kasar.

Wannna biki dai dadaddiyar al'ada ce da aka fara samar da ita a shekarar 1876, to amma a shekarar 2018 gwamnatin Japan ta ayyana ta a matsayin doka tare da rage shekarun budurcin daga 20 zuwa 18 don haka biki na gaba da za a yi shi ne a shekarar 2022.

A wannan shekarar an samu karuwar 'yan mata idan aka kwatanta da shekarun baya, kuma mun tsakuro muku kadan daga cikin kayatattun hotunan 'yan matan cikin kwalliya ta musamman dan wannan rana.

Mun zabo muku wasu daga cikin kayatattun hotunan bikin na bana.