Saudiyya za ta kara haraji ga fasinjojin jiragen sama

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumomi a Saudiyya za su kara kudaden haraji ga fasinjojin jiragen sama da ke zirga-zirga a cikin kasar daga farkon shekarar 2020.

Hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar wacce za ta kakaba wannan tara ta kasa da dalar Amurka uku, ta ce za a yi amfani da kudin ne wajen kula da ingancin jiragen saman.

Sai dai wannan tara ba ta shafi jarirai da fasinjojin jirgin yawo da kuma ma'aikatan jirgin ba.

Wannan matakin, irinsa na farko, na zuwa ne yayin da gwamnatin kasar ke fuskantar gibin sama da dala biliyan 50 a shekara mai zuwa kimanin kashi shida cikin 100 na abin da kasar ke samarwa a shekara ta fannin tattalin arzikinta.

Harin da aka kai wa matatun mai na Saudiyya a kwanakin baya na daya daga cikin abubuwan da kan iya shafar tattalin arzikin kasar.

Ko a kwanakin baya sai da kamfanin tace mai na kasar wato Saudi Aramco ya ce harin ya sanya man da kasar ke samarwa ya yi kasa da ganga miliyan 5.7 a kowace rana.

A 'yan kwanakin nan dai Saudiyya na ta fito da sabbin hanyoyin samun kudin shiga domin rage dogaro da arzikin danyen man fetur wanda take da shi.

Cikin tsare-tsaren harda bude kofofinta ga masu sha'awar zuwa can domin yawon bude idanu daga kasashen duniya.

Haka zalika kasar a kwanakin baya ta gayyaci fitattun mawaka na duniya domin rakashewa ta fannin nishadi. Hakan ya jawo rudani matuka musamman ga masu kallon kasar a matsayin kasa da wasu kasashe ke koyi da ita ta bangaren addinin musulunci.

Yarima Mohammed bin Salman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima Mohammed bin Salman

Tattalin arziki

Yarima mai jiran gado, Mohammad bin Salman ya ce yana son yin sauye-sauye a kasar ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki a wani bangare na ganin Saudiyyar ta tafi dai-dai da zamani da aka yi wa lakabi da Vision 2030.

Kasar Saudiyya dai ta dogara ne kan man fetur to amma kasancewar tangal-tangal din da aka samu a farashin man a kasuwar duniya ya sanya Saudiyyar tunanin dogaro da man babu tabbas.

Sakamakon bukatar kasar ta ganin an samu sauye-sauye a tattalin arzikin kasar musamman shigar masu zuba jari, Saudiyya take ta kokarin ta nuna wa duniya cewa kofofinta a bude suke ga 'yan kasuwa.