Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yara 12,500 sun mutu a Afghanistan a shekara 4
Kungiyar kare hakkokin yara ta Save the Children ta ce cikin shekaru 18 da aka kwashe ana yaki tsakanin kawancen da Amurka ke jagoranta kan 'yan Taliban babu abin da yaran kasar suka sani face tashin hankali.
Save the Children ta ce yaran na rayuwa cikin firgici da tsananin tsoro, ya yin da kashi 80 cikin 100 wadanda suka shaida tashin bama-bamai da mutuwa yara ne 'yan kasa da shekara 18 kamar yadda mukaddashiyar daraktan kungiyar a Afghanistan Jasmine Jahromi ta shaidawa BBC.
Ta ce tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018, yara 12,500 aka kashe, kuma kaso mafi tsoka na wannan adadin a bara aka kashe su, a bayyane ta ke tashin hankali na kara munana a kasar nan.
Jasmine ta kara da cewa wasu lokutan ana kashe yaran ko ji musu rauni ne sakamakon wajen da suke zaune da iyayensu mai cike da hadari ne.
Ta kara da cewa ''Akwai lokutan da ake kai hare-hare makarantu da asibitoci, ko a shekarar da ta gabata sama da makarantu 700 aka rufe sakamakon tashin hankali da ya munana a Afghanistan. Watanni biyu da suka wuce, an harba makaman roka kan wasu azuzuwan daukar karatu da Save the Children ta samar dan koyawa yara karatu, ana cin zarafin jami'an lafiya hakan ta sa dole muka rufe asibitocinmu. A kasa irin wannan kullum cikin hadari ka ke, ba ka san abin da zai same ka ba idan ka na tafiya.''