Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd ta yi wasanta mafi muni na waje a shekara 30
Manchester United ta yi wasa mai kyau amma an hana mu fanareti a wasan da muka yi canjaras na Europa da AZ Alkmaar in ji kociyanta Ole Gunnar Solskjaer, yayin da alkaluma ke nuna cewa shi ne wasanta na waje mafi muni a shekara 30.
Kociyan ya fadi hakan ne kuwa duk da yadda ta kasance a zahiri kungiyar ta Premier ba ta tabauka wani abin a-zo-a-gani ba a wasan.
United ba ta hari ragar abokan karawar tata ba ko da da bal guda daya a wasan maras armashi.
Sakamakon ya sa yanzu Man United ta kasa yin nasara a wasanninta 10 na waje.
To amma duk da wannan ci-baya kociyanta Solskjaer ya ga wasan a matsayin wani ci-gaba, har ya mayar da hankali kan fanaretin da yake ganin ya kamata a ba wa kungiyar tasa, lokacin da Stijn Wuytens ya kayar da Marcus Rashford saura minti 10 a tashi.
Alkalin wasa bai bayar da fanaretin ba, kuma ya kasance ba a amfani da hoton bidiyon fasahar VAR da ke taimaka wa alkalin wasa warware takaddama a matakin wasannin rukuni na gasar cin kofin na Europa.
AZ ta samu dama fiye da United, inda alkalin wasa ya hana bal din da dan wasanta na gaba Myron Boadu ya ci da cewa ya yi satar gida.
Man United ta samu koma kasancewar ta kammala wasan da mutum goma sakamakon Lingard ya ji rauni a cinyarsa, abin da ya sa ya yi waje.
Solskjaer na tsammanin da wuya dan wasan ya warke har ya iya taka leda a karawar da za su yi ta Premier ranar Lahadi da Newcastle.
Yanzu dai United tana da maki hudu daidai da Partizan Belgrade a saman rukuninsu na 11 (Group L).
Kungiyar ta Serbia ta ci wasanta 2-1 a Astana, tun kafin wasan na United, ranar Alhamis, inda Umar Sadiq ya daga raga har sau biyun.
Fafutukar United:
Yanzu dai Manchester United ba ta yi nasara ba a duk wani wasanta na waje tun bayan da ta doke Paris St-Germain a wasan Zakarun Turai na, Champions League a watan Maris.
A karon farko Manchester United ta kasa kai hari da bal ta nufi raga daidai a gasar Europa, a wasanni 25.
David de Gea ya tsare ragarsa, ba a daga ta ba a karon farko a Manchester United, tun wasan da suka yi da Fulham a watan Fabrairu, inda ya kawo karshen jefa masa bal a raga a wasanni goma na waje.