Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
WHO: Tanzania na boye bayani kan Ebola
Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce kasar Tanzania na kin bada cikakken bayani kan wasu da ake zargin suna dauke da cutar Ebola, inda hakan ke kawo cikas a yakin da ake yi da cutar.
WHO ta ce ta samu bayanan akwai mutum biyu da suka kamu da cutar daya a birnin Dar es Salam daya kuma a Mwanza.
Amma a kwanakin baya ministar lafiyar Tanzania Mis Ummy Mwalimu ta ce mutane biyu da aka yi wa gwajin jini an tabbatr ba su da cutar.
Sai dai a yanzu hukumar lafiyar ta ce ba bu wata shaida ko sakamakon gwajin jinin da aka ba ta a hukumance.
Barkewar cutar Ebola ta baya-bayan nan ta hallaka sama da mutane 2,000 a jamhuriyar dimukradiyyar Congo.
A bangare guda aikin hana yaduwar cutar kasashe makoftaka na ci gaba da zama barazana musamman a yankuna da ake fuskantar tashin hankali.