Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Congo za ta fitar da sabuwar rigakafin Ebola
Hukumomi a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo na shirin fara amfani da rigakafi ta biyu domin dakile cutar Ebola da ta kashe sama da mutum 2100.
A watan Yuli, tsohon Ministan Lafiya na kasar Oly Ilunga ya ki amincewa da amfani da rigakafin, inda ya ce ba a tabbatar da ko rigakafin za ta yi aiki ba.
Sai dai jami'an lafiya a kasar sun bayyana cewa rigakafin, wadda kamfanin samar da magunguna na Johnson & Johnson suka hada, ba ta da wata illa.
Barkewar cutar Ebola a gabashin kasar ita ce ta biyu mafi girma.
Barkewar cutar da ta fi grima ta faru ne tsakanin 2015 zuwa 2016 a yammacin Afirka, inda ta kashe sama da mutum 11,000.
Rigakafin da Johnson & Johnson suka samar, za ta tamaka wa rigakafin da kamfanin Merck suka samar wadda tuni aka bai wa mutum 225,000 a bara, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar.
Sai dai jami'an da ke kula da bullar cutar ba su bayyana takamaiman lokacin da za a fara amfani da rigakafin ba.
Rigakafin da ake amfani da ita yanzu a kasar ba ta da yawa, an bayyana cewa ma'aikatan lafiya ne kadai ke amfani da ita sai kuma mutanen da ake ganin suna da yiwuwar kamuwa da cutar sakamakon cudanya da masu dauke da ita.
Ana sa ran sabuwar rigakafin za ta samar da kariya matuka, inda har wadanda ke wurin da cutar ta barke za su samu rigakafin.