'Abin da ya sa mutane ba sa tsawon rai a Chadi idan aka kwatanta da Finland'

Ana iya amfani da inda aka haife ku a yi hasashen yadda rayuwarku za ta kasance a gaba, domin haka yaron da aka haifa a kasar Chadi ya fi takwaransa na kasar Finland saurin yiwuwar mutuwa har sau 53.
Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoton mai taken 2019 GoalKeepers wanda Gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation ta wallafa da ke magana kan manyan rashin daidaito tsakanin kasashe da yankuna musamman ma a nahiyar Afirka.
Rahoton ya kuma yi nunin cewa harkokin gina dan'adam da suka hadar da lafiya da ilmi a matsayinsu na muhimman bangarori, sun bunkasa da kashi 99 cikin dari na larduna a kasashe masu tasowa cikin shekara 17 da ta wuce.

Asalin hoton, Others
Kan yadda za a iya inganta ci-gaban da aka samu domin samun nasarar muradan ci-gaban karni.
Bill Gates, shugaban Gidauniyar Bill & Melinda Gates ya shaida wa BBC cewa muhimmin abu na farko don ganin an rage mutuwar kananan yara shi ne, bunkasa tsarin kula da lafiya matakin farko. Ya ce a wannan ba wai batun likitoci ba ne ko samar da asibitoci kadai ba.
Ya ce abu ne na samun ma'aikatan da za su ilmantar da iyaye mata kan muhimmancin zuwa awo da kula da lafiyar jarirai da alluran riga-kafi da kuma dabarun sarrafa abinci mai gina jiki.
Mista Gates ya ce saboda haka akwai hanyoyi biyu da za a tabbatar da hakan:
Hanya ta farko ya ce, ya kamata a kalli kasashe da ba sa samun kudade sosai a ga abin da suka yi ko suke yi a fannin kula da lafiya sai a yi koyi da su.
Hanya ta biyu kuwa ita ce, mutum ya duba a cikin kasarsa wane sabon abu ne ga masu shirya rahoton GoalKeepers, misali a Najeriya ko India, ''kana da abubuwa da suka sha bamban, idan har za a kalli wannan to za a samar da sauyi.''

Dangane da kasashen da yake ganin suna kokari sosai a harkar kula da lafiya, attajirin ya ce, kasashe kamar Ethiopia da Rwanda da Tanzania sun yi matukar kokari a harkar kula da lafiya matakin farko.
Su kuwa kasashen da suke nawa kuwa Mista Gates ya ce sun kunshi dukkanin kasashen yankin Sahel.
Ya kara da cewa kamar a arewacin Najeriya za a samu adadi mafi yawa a yaran da ake haifa suke mutuwa.
Ya ce amma a daukacin yankin kasashe irin su Chadi da Nijar ana samun yara fiye da kashi 10 cikin dari wadanda ake haifa suna mutuwa.
Da aka nemi ya kwatanta bambancin kyawun rayuwa tsakanin matar da take a Chadi da kuma wadda take a Finland, Bill Gates, ya ce lamarin abin tausayi ne matuka.
Ya ce, amma idan kasashe suna kara samun wadata ratar da ke ratar da ke tsakanin jinsina tana kara raguwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ya kara da cewa, ko a kasashe kamar Amurka suna da sauran aiki, to amma wan abu shi ne ayyukan wahala da rashin 'yanci da rashin samun ilimi da mata ke fuskanta abin ya yi muni a matalautan kasashe.
Saboda haka yana ganin ya kamata a inganta hanyoyin samun kudaden mata.
Ya ce taimaka wa mata yana da gagarumin amfani saboda idan suka samu ilimi za su iya neman kudi da tallafa wa 'ya'yansu.
Sannan kuma ya ce, za su so yin haihuwa kadan saboda sun samu ilimi in ji Bill Gates din.











