Premier League: Liverpool ta kafa tarihi a Ingila

Asalin hoton, @LFC
Liverpool ta kafa tarihi a gasar Premier bayan wasan da ta lallasa Newcastle da ci 3-1 a wasan Premier mako na biyar ranar Asabar.
Tawagar Jurgen Klopp din ta yanke shawarar dorawa daga inda ta tsaya bayan dawowa daga hutun League na mako daya da aka yi.
Jetro Willems na Newcastle ne ya fara zura kwallo a ragar masu masaukin bakin a filin wasa na Anfiled a minti na 7.
Daga bisani kuma Sadio Mane ya farke ya kuma kara, sannan Mohammed Salah ma ya zura tasa.
Wannan nasara ta mayar da Liverpool kungiya ta farko a Ingila da ta ci wasa 14 a jere tare da cin kwallo sama da daya a dukkanin wasannin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi ma Sadio Mane ya kafa nasa tarihin, inda ya zama dan wasa na farko da ya buga wa kulab guda daya wasannin Premier a gida har guda 50 ba tare da ya yi rashin nasara ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Sai kungiyoyin Premier sun yi da gaske kafin su cimma Liverpool din ganin irin wutar da take yi a baya-bayan nan.
Shekara 30 kenan rabon da kungiyar lashe kofin Premier.
Sai dai taurarin 'yan wasan gabanta wato Mane da Salah da Firmino sun kai kungiyar kusa da kofin Premier a bara, tare da niyyar bana za su kara kusanci da kofin.
Yanzu haka dai Liverpool ta yi wasa 22 a Premier a jere ba tare da rashin nasara ba.