Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cutar Ebola ta sake bullowa a yammacin Uganda
Ma'aikatar lafiya a Uganda ta tabbatar da sake bullar cutar Ebola a yammacin garin Kasese.
An gano cutar ne bayan an gwada jinin wata karamar yarinya 'yar shekara 9, da ta taho daga Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, inda aka ga tabbas tana dauke da cutar.
Cutar na saka masassara mai zafi da kuma zubda jini.
Tuni dai aka kebe yarinyar inda aka ajiye ta a cibiyar kula da kuma shan magani ta Ebola a kasar.
Kasar ta Uganda tana matsa kaimi wajen tantancewa da kuma gwaje-gwaje ga mutanen da ke shiga kasar ta kan iyakarta, da jamhuriyyar dimokradiyyar Kongo sakamakon yadda cutar ta kashe kusan mutum dubu 2 a Kongon.